Zan ci gaba da addu'a Allah yasa Musulmai su ginawa kiristoci Coci, Bishop Kukah
- Bishop Mathew Kukah ya bayyana cewa, yana ci gaba da addu'ar Allah yasa wata rana Musulamai su gina Coci ga Kiristoci
- Bishop din ya yi wannan batu ne a taron kaddamar da rukunin gidajen da wani Cocin katolika ya gina ciki har da masallaci ga Musulmai
- Ya kuma yi kira ga gamnatin jihar Adamawa da ta jawo hankalin sauran gwamnoni a kasar don wanzar da zaman lafiya
Bishop din Cocin Katolika na Sakkwato, Rev. Matthew Kukah, ya ce zai ci gaba da addu’a wata rana Musulmai ko za su gina wa Kiristoci coci.
Mista Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ake kaddamar da rukunin gidaje 86 tare da coci da masallaci ga 'Yan Gudun Hijira a kauyen Sangere-Marghi da ke karamar Hukumar Girei a Jihar Adamawa.
KU KARANTA: Sakon Buhari ga Musulmai a Ramadana: Ku guji a ingizaku zuwa raba kawunanku
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa musulmai da kirista duka sun ci gajiyar gidajen da Rev. Stephen Dami Mamza, Bishop din Cocin Katolika na Yola ya gina.
Mista Kukah ya ce bai kamata a rasa mahimmancin gina rukunin gidajen da masallacin ba.
“Ya kamata 'yan Najeriya su koyi yin addini da hakuri da kauna ga makwabtansu.
"Yana da muhimmanci Krista da Musulmai su yaba da abin da Faston na Yola ya yi a yau," in ji Mista Kukah.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sake kai farmaki yankin Kaduna, sun sheke mutane biyar
A wani labarin, Bishop na cocin Katolika na Yola, Revd. Fr. Stephen Mamza, ya bayyana cewa ya gamu da adawa lokacin da ya bayyana aniyarsa ta gina masallaci ga Musulmai 'Yan Gudun Hijira a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Mamza, wanda ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Punch, ya ce da farko, ba su nuna wariya ga kowa ba lokacin da shi da sauran mambobin cocin suka dauki bakuncin 'yan gudun hijira.
Legit.ng ta tattaro cewa malamin ya ce ba su tambayi addinin da ‘yan gudun hijirar ke bi ba ko kuma su nemi cocinsu da suke bauta, ya kara da cewa an dauki 'yan gudun hijirar a matsayin ’yan Adam da ke bukatar taimako.
Asali: Legit.ng