Buhari: Korona ta budewa masana kimiyya a Najeriya baiwar kirkira

Buhari: Korona ta budewa masana kimiyya a Najeriya baiwar kirkira

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa Injiniyoyi a kokarin da suka yi wa a yaki da Korona

- Shugaban ya kuma bayyana cewa, idan aka tallafawa kokarin nasu zai haifar da mai ido nan kusa

- Hakazalika ya yaba wa mambobin Kwalejin Injiniyanci ta Najeriya a yayin gabatar da wani taro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce annobar Korona ta bayyana irin karfi, baiwa da kuma kirkirar da masana a kasar ke dashi, Daily Trust ta ruwaito.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron tattaunawa da Kwalejin Injiniyanci ta Najeriya ta shirya, shugaban ya yaba wa injiniyoyin Najeriya kan nuna gogewa da kwarewarsu.

Buhari, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, SAN, ya yaba wa makarantar da membobinta.

A cewarsa, "Ina ganin hakika annobar ta bude babbar baiwa da kere-kere ga masana kimiyya da injiniyoyi a Najeriya kuma idan har aka tallafawa halin a yanzu, to 'yan shekaru masu zuwa na iya zama abin birgewa."

KU KARANTA: Zan ci gaba da addu'a Allah yasa Musulmai su ginawa kiristoci Coci, Bishop Kukah

Buhari: Korona ta budewa masana kimiyya a Najeriya baiwar kirkira
Buhari: Korona ta budewa masana kimiyya a Najeriya baiwar kirkira Hoto: akelicious.net
Asali: UGC

“Muna alfahari da Kwalejin Injiniyanci ta Najeriya; membobin ku sun hada da kwararrun injiniyoyin Najeriya a duk bangarorin masana'antu na injiniyanci a Najeriya da kuma kasashen waje.

"Wannan yana ba da zurfi da nuna gogewa da kwarewa don ba da shawara kan kusan dukkanin bangarorin injiniya a kasar."

Yayin da yake magana kan mahimmancin Kimiyya, Fasaha da Injiniyanci wajen magance annobar, Shugaban ya lura cewa duniya ta juya ga wadannan fannonin “don neman mafita da amsoshi cikin gaggawa.

"Ina da yakinin cewa a matsayinku na injiniyoyi, za ku yarda da ni cewa daya daga cikin mahimman darussa game da martani kan annobar ita ce mahimmancin dogaro da kimiyya da injiniyanci.”

Da yake tsokaci kan damarmakin da aka samu a lokacin kulle a kasar, Shugaba Buhari ya ce "babbar dama ce ta kirkirar fasahohi masu inganci ga ayyukan zamani, ciki har da Telemedicine da Fintech."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sake kai farmaki yankin Kaduna, sun sheke mutane biyar

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya yi maraba da fara azumin watan Ramadana wanda za a azumta na tsawon kwanaki 30, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin sakon da ya aike wa 'yan kasar na Ramadan, Buhari ya roki Allah da ya karbi "sadaukarwar da muka yi ya kuma kara hadin kai, kaunar juna, zaman lafiya da ci gaban kasar."

Buhari, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bukaci musulmin kasar da su yi hakuri da juriya tare da yin watsi da muryoyin da ke neman raba kan al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel