Yanzu Yanzu: Gwamna El-Rufai da Fasto Adeboye sun gana a Kaduna

Yanzu Yanzu: Gwamna El-Rufai da Fasto Adeboye sun gana a Kaduna

- Gwamna El-Rufai ya gana da shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto Adeboye

- Sun yi ganawar ne a gidan Gwamnati na Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna a yau Talata, 13 ga watan Afrilu

- Zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan abubuwan da suka tattauna

Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto Enoch Adeboye, a ranar Talata, ya gana da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

An yi ganawar ne a gidan Gwamnati na Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Gwamnatin Kaduna ta sanar da batun ganawar shugabannin biyu a shafinta na Instagram.

Ganawar na zuwa ne kwanaki bayan babban faston mai shekaru 79 ya bayyana cewa an saki mambobin cocin guda takwas da aka sace a Kaduna.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an kaiwa mambobin RCCG a Kaduna hari a ranar 26 ga Maris a kusa da Doka kan hanyar Kachia-Kafanchan, akan hanyarsu ta zuwa wani taro.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane 40 hade da wadanda suka yi garkuwa da ma'aikatan hukumar kare hadurra FRSC.

Kwamishinan yan sanda jihar, Bola Longe ne ya sanar da haka ranar Litinin yayin wani taro da aka yi da sarkunan gargajiya, shugabannin karamar hukuma da hafsoshin tsaro a Lafia, babban birnin jihar.

Gwamnan jihar, Abdullahi Sule ne ya jagoranci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng