Yan sanda sun damke yan bindigan da suka yi garkuwa da ma'aikatan FRSC

Yan sanda sun damke yan bindigan da suka yi garkuwa da ma'aikatan FRSC

-Wasu masu garkuwa da mutane 40 sun shiga hannun yan sandan jihar Nasarawa

-Daga cikin masu garkuwar akwai wadanda suka yi garkuwa da ma'aikatan hukumar kiyaye hadurra

-Kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanar da haka ranar Litinin a garin Lafiya

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane 40 hade da wadanda suka yi garkuwa da ma'aikatan hukumar kare hadurra FRSC.

Kwamishinan yan sanda jihar, Bola Longe ne ya sanar da haka ranar Litinin yayin wani taro da aka yi da sarkunan gargajiya, shugabannin karamar hukuma da hafsoshin tsaro a Lafia, babban birnin jihar.

Gwamnan jihar, Abdullahi Sule ne ya jagoranci taron.

"Mun kama kimanin masu garkuwa da mutane 40 kuma muna bincike a kansu. Mun kuma kame wadanda suka yi garkuwa da ma'aikatan hukumar kare hadurra FRSC a Maraban."

"Wasu daga cikin ma'aikatan hukumar sun zo ne daga Sokoto da Abuja kuma sun bayyana irin yan ta'addan da suka yi garkuwa da su," Cewar kwamishinan.

KU KARANTA: Yanzun nan: Shugaba Buhari ya yi wani nadi mai muhimmanci

Yan sanda sun damke yan bindigar da suka yi garkuwa da ma'aikatan FRSC
Yan sanda sun damke yan bindigar da suka yi garkuwa da ma'aikatan FRSC Source: Twitter
Asali: Twitter

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

Ya kuma bada tabbacin hadin kai da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro a cikin jihar.

Anyi garkuwa da ma'aikatan ne a watan satumban 2020 a motar bas yayin da suka fito daga jihar Sokoto da Kebbi, kan hanyarsu ta zuwa wani horo a makarantar hukumar kiyaye hadurra dake Udi, Abuja.

An rahoto an sace su a Udege, kan hanyar Mararaban-Udege a jihar Nasarawa, misalin karfe 8 na safe. Harin yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin ma'aikatan sannan daya ya mutu a asibiti, hudu kuma sun jigata.

Mai magana da yawun hukumar, Bisi Kazeem ta tabbatar da tsirar takwas daga cikinsu ba tare da rauni ba sannan kuma yan ta'addan sunyi garkuwa da goma.

A bangare guda, kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng