Yanzun nan: Shugaba Buhari ya yi wani nadi mai muhimmanci
- Shugaban kasa Buhari ya sabonta nadin Farfesa Bissallah Ahmed Ekele, a matsayin Shugaban likitoci (CMD) na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja (UATH)
- Hakan ya biyo bayan muhimmiyar rawar ganin da Ekele ya taka wajen kawo ci gaba a wa'adinsa na farko
- Sabon nadin zai yi aiki ne na tsawon wasu shekaru hudu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Farfesa Bissallah Ahmed Ekele, a matsayin Shugaban likitoci (CMD) na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja (UATH), Gwagwalada, Abuja.
Wata sanarwa da aka bai wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata, ta bayyana cewa nadin Farfesa Ekele zai yi aiki na wa’adin shekaru hudu bayan sadaukar da kai da yayi a farkon wa’adin shugabancinsa.
KU KARANTA KUMA: Ka gyara titunan da suka hada manyan kananan hukumomi a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum
Yayin da yake taya shi murnar sake nada shi, Buhari ya bukaci Ekele da ya yi amfani da nauyin da aka daura mashi wajen ci gaba da bunkasa asibitin da kuma bangaren kiwon lafiya a kasar.
“Farfesa Ekele ya karbi aiki a hukumace daga hannun mukaddashin CMD, Dr A.S. Haruna, a ranar 3 ga watan Yulin, 2017, kuma ya taka rawar gani a ci gaban ababen more rayuwa, bincike, aiyukan asibiti da sauransu,” in ji sanarwar.
KU KARANTA KUMA: Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami
A wani labarin kuma, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.
Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.
Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.
Asali: Legit.ng