Ka gyara titunan da suka hada manyan kananan hukumomi a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum

Ka gyara titunan da suka hada manyan kananan hukumomi a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum

- Rundunar Sojoji ta yaba da taimakon Farfesa Babagana Zulum

- A sakamakon wannan, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya ce gwamnan ya taimaka masu sosai a fannin kayan aiki

- Attahiru ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa Sojojin za su yi komai don fatattakar masu tayar da kayar baya

Shugaban hafsin sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya yabawa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum saboda tallafawa sojojin Najeriya musamman a fannin kayan aiki.

Janar Attahiru ya ce tallafin ya inganta aikin Operation Lafiya Dole tare da alherin da ya yi wa iyalan sojojin da suka mutu.

KU KARANTA KUMA: Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami

Ka gyara titunan da suka hada babbar karamar hukuma a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum
Ka gyara titunan da suka hada babbar karamar hukuma a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne lokacin da Gwamnan jihar Borno ya kai masa ziyarar girmamawa a Hedikwatar Sojoji, Abuja.

Janar Attahiru ya ba Gwamnan tabbaci kan aniyar Sojojin Najeriya a karkashin jagorancinsa na fatattakar duk masu adawa da kuma dawo da zaman lafiya a kasar.

Ya sanar da Gwamnan cewa “wata tawaga da ta kunshi manyan ma’aikata a Hedikwatar Sojoji da Kwamandojin rundunar sun kasance a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, don tantance bukatun sojojin da nufin magance su.”

KU KARANTA KUMA: Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC

Shugaban sojojin ya kuma yi kira ga Gwamnan da ya aiwatar da gyare-gyare a kan titunan da suka hada manyan Kananan Hukumomin jihar domin bawa sojoji damar gudanar da ayyukansu tare da mafi karancin matsaloli.

Kawo karshen ta'addanci

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yabawa rundunar sojojin Najeriya (NA) saboda himma da jajircewarta wajen kawo karshen ta'addanci a yankin arewa maso gabas da sauran kalubalen tsaro a kasar.

Gwamna Zulum ya ce "sun kawo ziyarar ne don taya COAS murnar nadin nasa wanda ya cancanta kwarai da gaske, tare da tattaunawa a kan dabarun da za su taimaka wajen inganta ayyukan magance masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas."

A wani labarin, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar Amurka ke zargi.

A daya daga cikin sakonninta, NewWireNGR ta yi zargin cewa Pantami yana karkashin kulawar Amurka saboda zargin alakarsa da mayakan Boko Haram, Abu Quatada al Falasimi, da sauran shugabannin kungiyar Al-Qaeda.

Ba wadannan kadai ba, jaridar ta yanar gizo ta yi ikirarin cewa Pantami, kafin nadin nasa, sanannen mai wa'azin addinin Islama ne wanda ke yada akida mai hatsari a kan gwamnatin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng