Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami

Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami

- Sheikh Isa Pantami, ministan sadarwa ya nesanta kansa daga zargin cewa yana cikin jerin wadanda Amurka ke sanya wa ido saboda ta'addanci

- Pantami ya jaddada cewa yana daga cikin malaman addinin Islama na farko da suka fara kalubalantar koyarwar marigayi shugaban kungiyar Boko Haram, Muhammed Yusuf

- Ya kuma bukaci da a janye rahoton a cikin awanni 24 a jaridun kasar biyar da kafofin watsa labarai biyar na duniya

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya yi tir da rahotannin da ke cewa an sanya shi a cikin jerin 'yan ta'adda a Amurka.

Ya ce babu wata kungiyar leken asiri da ta hada shi da wata kungiyar ta'addanci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC

Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami
Ban taba shiga jerin wadanda ake zargi da ta’addanci ba - Sheikh Pantami Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 12 ga Afrilu, 2021 kuma dauke da sa hannun Michael Numa Esq., Wacce aka aike wa jaridar Daily Independent Newspaper, Pantami ya bukaci da a janye rahoton a cikin awanni 24 a cikin jaridun kasar biyar da kafofin watsa labarai biyar na duniya.

Ya ce yana daga cikin malaman addinin Islama na farko da suka fara tattaunawa da marigayi shugaban kungiyar Boko Haram, Muhammed Yusuf, a wata muhawara ta gidan talabijin don kalubalantar koyarwarsa domin cewa ya saba wa Musulunci.

KU KARANTA KUMA: Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami

A baya mun ji cewa, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar Amurka ke zargi.

A daya daga cikin sakonninta, NewWireNGR ta yi zargin cewa Pantami yana karkashin kulawar Amurka saboda zargin alakarsa da mayakan Boko Haram, Abu Quatada al Falasimi, da sauran shugabannin kungiyar Al-Qaeda.

Ba wadannan kadai ba, jaridar ta yanar gizo ta yi ikirarin cewa Pantami, kafin nadin nasa, sanannen mai wa'azin addinin Islama ne wanda ke yada akida mai hatsari a kan gwamnatin Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel