Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC

Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC

- Matawalle na iya shan kaye a hannun manyan masu fada a ji na APC idan har ya koma jam'iyyar don neman zarcewarsa a 2023

- Duba ga rigingimun da ya faru a jam'iyyar APC a lokacin zaben 2019, idan har Matawalle ya koma cikinta, zai zama ya jingina kansa ga jam'iyyar da ke cikin rudani

- A yanzu haka akwai ikirarin cewa talakawa na jira su huce fushinsu kan gwamnatin da APC ke jagoranta da kuri’unsu a 2023

Duk da cewa har yanzu Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara bai fito fili ya bayyana niyyarsa ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba, amma akwai wasu dalilai masu karfi da za su iya yin aiki a kan shi, wanda ka iya sanadiyar rasa kujerarsa.

Yawancin waɗannan abubuwan, idan ba duka ba, sun riga sun wanzu a ciki da wajen jam’iyya mai mulki.

KU KARANTA KUMA: PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC
Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Facebook

1. Hukuncin kotun koli

A wani hukuncin Kotun Koli da Babban Alkalin Najeriya (CJN) Tanko Muhammad ya karanta, a cikin shekarar 2019, an umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta soke duk kuri’un da APC ta jefa a lokacin zaben gwamna kan gazawar jam’iyyar na gudanar da zaben fidda gwani.

Kotun kolin ta kuma umarci INEC da ta amince da ‘yan takarar jam’iyyun siyasa da suka zo na biyu (wanda ya kasance PDP) don su karbi mulki a matsayin ‘yan takarar da aka zaba.

Don haka, sauya sheka zuwa APC na iya barin Matawalle ya jingina kansa ga jam'iyyar da ba a san ta ba a zaben.

2. Rikicin shugabanci a APC

A yanzu haka, bangarori biyu masu hamayya da juna a babin jam’iyyar APC na jihar Zamfara karkashin jagorancin Abdulaziz Yari, wanda ya gabaci Matawalle, da kuma Sanata Kabiru Marafa sun kafa idanunsu kan kujerar gwamnan.

Akwai damar cewa Matawalle na iya shan kaye a hannun manyan masu fada a ji a yakin neman tazarcensa a 2023 idan a lokacin ya zabi sake tsayawa takara a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Zan bar Kaduna da zaran na kammala wa’adin mulkina - El-Rufai

3. Rikicin APC

Babu shakka cewa APC ta rasa yawancin farin jininta, musamman a arewa wacce ke fama da rikici iri-iri.

Har ila yau, Hakar ma'adanai ba bisa ka’ida ba da ya zama ruwan dare a Zamfara wanda gwamnatin tarayya ta dakatar da shi kwanan nan, hade da umarnin haramta tashin jirage da fadar shugaban kasa tayi, kamar yadda mafi yawan mazauna yankin ke kallon lamarin ba ita ce mafitar da za ta taimaka masu wajen fita daga yanayin da suke ciki ba.

Akwai ikirarin cewa talakawa na jira su huce fushinsu kan gwamnatin da APC ke jagoranta da kuri’unsu a 2023.

A zahiri, yanzu PDP na shirin cin gajiyar gazawar APC a zabuka masu zuwa.

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji AbulAziz Yari, ya bayyana cewa gwamna Bello Matawalle zai tashi a tutar babu idan har ya koma jam’iyyar APC.

Jaridar Punch ta rahoto Alhaji AbulAziz Yari ya na cewa Gwamna Bello Matawalle zai iya rasa kujerarsa, muddin ya sauya-sheka daga jam’iyyarsa ta PDP.

Babban jigon na APC, AbulAziz Yari ya bayyana cewa Bello Matawalle zai yi asarar kujerar gwamna idan aka yi la’akari da yadda ya samu mulki a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel