Karya kika yi, Amurka bata zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci – Hadimin Buhari ga kafar yada labarai

Karya kika yi, Amurka bata zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci – Hadimin Buhari ga kafar yada labarai

- NewWireNGR, kafar yada labarai ta gida, ta sha zazzafan caccaka saboda sabbin rahotannin ta akan Isa Pantami

- Jaridar ta yi ikirarin cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki yana cikin jerin wadanda Amurka take zargi da daukar nauyin ayyukan ta'addanci

- Sai dai mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmed ya karyata zargin kuma ya bayyana shi a matsayin kanzon kurege

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar Amurka ke zargi.

A daya daga cikin sakonninta, NewWireNGR ta yi zargin cewa Pantami yana karkashin kulawar Amurka saboda zargin alakarsa da mayakan Boko Haram, Abu Quatada al Falasimi, da sauran shugabannin kungiyar Al-Qaeda.

KU KARANTA KUMA: Jerin abubuwa 3 masu karfi da ka iya sa Matawalle ya rasa kujerarsa idan ya koma APC

Karya kika yi, Amurka bata zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci – Hadimin Buhari ga kafar yada labarai
Karya kika yi, Amurka bata zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci – Hadimin Buhari ga kafar yada labarai Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Ba wadannan kadai ba, jaridar ta yanar gizo ta yi ikirarin cewa Pantami, kafin nadin nasa, sanannen mai wa'azin addinin Islama ne wanda ke yada akida mai hatsari a kan gwamnatin Amurka.

Sai dai kuma, a cikin sakonsa na Twiter a ranar Litinin, 12 ga Afrilu, Ahmad ya yi watsi da ikirarin a matsayin karya, yana mai cewa gidan yada labaran ta cikin gida da gangan ta kauce don tabbatar da gaskiyar lamarin sannan ya ci gaba da yaudarar dimbin makaranta yan Najeriya.

Ya ce:

"Yanzu nan kin yada rahoton karya ba tare da tabbatarwa ba. A matsayin ki na kafar yada labarai @NewsWireNGR kin san yadda ake tabbatar da irin wadannan rahotannin, amma a'a, kina nan kina yada labarin karya da hadari ga dubban mabiyan ki. FYI @DrIsaPantami bai taɓa kasancewa a cikin jerin mutane da Amurka ke sawa ido ba."

Don saita bayanan kai tsaye, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, ya ci gaba da cewa ministan bai taba kasancewa cikin jerin wadanda ake zargi a Amurka ba kamar yadda gidan yada labaran ta rahoto.

KU KARANTA KUMA: Wike ga 'yan siyasa: Talakawa sun gaji, ku daina yi musu alkawuran karya

A wani labari na daban, Mutane akalla shida aka kashe, sannan an raunata wasu da-dama a lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai hari a garin Damasak, jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa sojojin Boko Haram tare da kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP su ka kai wannan hari a karamar hukumar Mobbar.

Rahotannin sun tabbatar da cewa an kai wadannan hare-haren ne a ranar Asabar, 10 ga watan Afrilu, 2021, wanda ya yi sanadiyyar raunata wasu sojojin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng