Yanzu-Yanzu: An ji ƙarar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun

Yanzu-Yanzu: An ji ƙarar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun

Mutane sun shiga hargista a wurin taron jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen yankin Kudu maso yamma da aka gudanar a Osogbo babban birnin jihar Osun a a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 6.45 na yamma a lokacin da wasu da ake zargin yan bindiga suka matsa kuda da kofar shiga wurin taron na WOCDIF event centre suka yi kokarin kutsawa.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya bayyana dalilansa na rage ma'aikata a Kaduna

Yanzu-Yanzu: An ji karar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun
Yanzu-Yanzu: An ji karar harbe-harben bindiga a yayin da Fayose ke barin wurin taron PDP a Osun
Asali: Original

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yana daf da barin wurin taron ne sai yan daban suka yi yunkurin kustawa cikin wurin taron.

KU KARANTA: Yanzun nan: An kawo gawarwakin sojoji 12 makabarta don musu jana'iza a Benue

Jami'an tsaro sun dakile yunkurin kutsen da taimakon kwamishinan rundunar yan sandan jihar Osun, Olawole Olokode da wasu jami'an.

Jami'an tsaro sun ta yin harbe-harbe a sama domin fatattakar yan daban.

Jami'an tsaro sun fice da Fayose cikin wata mota kirar Jeep mai bakaken gilashi ba tare da wani abu ya same shi ba.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164