Nasara daga Allah: ‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka sace a jihar Kaduna

Nasara daga Allah: ‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka sace a jihar Kaduna

- Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar ceto mutane 15 daga hannun 'yan bindiga

- Sun kuma fatattaki gungun 'yan bindigan tare da raunata wasu daga cikinsun da suka tsere

- Hakazalika rundunar ta 'yan sanda ta samu nasarar kwato wasu shanu sama 32 a hannunus

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ceto mutane 15 da aka sace tare da kwato shanu 32, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Kaduna.

Jalige ya ce a ranar 9 ga Afrilu da misalin karfe 3:25 na yamma, wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Buruku Birnin Gwari da ke kusa da dajin Unguwan Yako a kokarinsu na yin garkuwa da mutanen da ke cikin a motoci guda biyu kirar Volkswagen.

KU KARANTA: A yau kasar Saudiyya za ta fara duban watan Ramadana mai zuwa

Nasara daga Allah: ‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka sace a jihar Kaduna
Nasara daga Allah: ‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka sace a jihar Kaduna Hoto: thenewspeak.com.ng
Asali: UGC

“Martanin da rundunar ta yi nan take ya tilasta wa 'yan bindigan suka tsere zuwa daji tare da samun raunin harbin bindiga, suka yi watsi da wadanda abin ya rutsa da su.

"Jami'an sun yi bincike a yankin baki daya kuma sun yi nasarar kubutar da mutane 15 ba tare da rauni ba," in ji shi.

Ya ce direbobin motocin sun samu raunuka daban-daban kuma suna karbar kulawar asibiti.

Jalige ya ce sauran wadanda abin ya rutsa dasu an tantance su sannan kuma sun hadu da danginsu.

Ya ce tsananin sintiri da kuma farautar 'yan bindiga da suka gudu ya kasance babban abinda rundunar ta sa a gaba.

Ya ce a ranar 8 ga watan Afrilu, da misalin karfe 5:00 na safe, rundunar ta samu wani rahoton sirri wanda ke nuna cewa an ga wasu ‘yan bindiga a kusa da kauyen Dutsin Gaya da ke cikin Karamar Hukumar Kajuru (LGA), suna kora garken shanu.

‘Yan sanda da suka samu labarin, an tura 'yan sanda zuwa yankin tare da fafatawa da ‘yan bindigan wanda ya tilasta musu tserewa da raunin harbin bindiga yayin da jami’an suka kwato shanu 32 da suka sace.

KU KARANTA: Bayan share shekaru 30 yana mulki, ana sa ran Idris Derby zai sake lashe zabe

A wani labarin daban, Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kuɓutar da mutane 11 daga hannun yan bindiga a jihar, Punch ta ruwaito.

Kakakin runduɓar ta yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a Gusau, babban Birnin jihar.

Ya ce a ranar 9 ga watan Afrilu hukumar yan sanda tare da taimakon ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar sun kuɓutar da wasu mutane 11 da wata tawagar yan bindiga ta sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel