Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai

Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai

- An tura sojoji wani yanki da ya yi iyaka da jihohin Ebonyi da kuma Benuwai don dawo da zaman lafiya a yankunan bayan ɓarkewar rikici.

- Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzun haka gwarazan sojin na can na fafatawa da yan bindiga a yankin

- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Ebonyi ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace basa zargin kowa sai mutanen garin Angila dake jihar Benuwai

Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzun haka gwarazan sojojin ƙasar nan na can suna fafatawa da wasu yan bindiga a iyakar dake tsakanin jihohin Ebonyi da kuma Benuwai.

KARANTA ANAN: Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Ana tsammanin sojojin na musayar wuta ne a yankin Agila dake jihar Benuwai wanda ya haɗa iyaka da garin Ngbo dake ƙaramar hukumar Ohaukwu, jihar Ebonyi.

Sai dai yan kunan biyu na fama da rikice-rikice na tsawon shekaru.

Mutane da yawa sun rasa rayukansu kuma an salwantar da ɗunbin dukiya a faɗace-faɗacen dake yawan faruwa tsakanin al'ummar yankunan biyun.

Lokacin da jaridar Dailytrust ta tuntuɓi kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Ebonyi, Stanley Okoro Emegha, da misalin ƙarfe 12:30 na rana, ya tabbatar da lamarin.

Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai
Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa

Ya ce: "Amma muna zargin waɗanda suka kai harin ba yan bindiga bane, muna zargin al'ummar Angila ne daga jihar Benuwai. Saboda sanannen abu ne mutanen mu da suka haɗa iyaka da su, suna samun matsaloli da su."

"Har yanzun babu adadin mutanen da harin ya shafa, sai dai mu jira muji daga gare su nan gaba."

Hakanan kuma kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Garba, ya bayyana ma manema labarai cewa ya tura jami'an yan sanda wurin da abun ke faruwa don dawo da zaman lafiya.

A wani.labarin kuma Bayani Dalla-Dalla kan Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara sayar da fom ranar Asabar ɗin da ta gabata.

JAMB ta dakatar da fara yin rijistar ne tun baya saboda wasu matsaloli da ba'a yi tsammani ba a kan lambar zama ɗan ƙasa NIN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel