Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

- Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadana daga ranar Litinin

- Sarkin ya bada wannan umarnin ne ta hanyar shugaban kwamitin bada shawara kan al'amuran addinin musulci na fadarsa dake Sokoto

- Daga ƙarshe shugaban kwamitin fadar sarkin ya bada lambobin waya da za'a iya kai rahoton ganin watan kai tsaye zuwa ga fadar Sarkin.

Sarkin musulmi dake jihar Sokoto, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci al'ummar musulman ƙasar nan da su fara neman jinjirin watan Ramadana na shekarar 1442AH daga ranar Litinin.

KARANTA ANAN: A yau kasar Saudiyya za ta fara duban watan Ramadana mai zuwa

Sarkin Musulmin ya bada wannan umarnin ne yau Lahadi a wani saƙo da shugaban kwamitin shawara kan al'amuran addinin Musulunci, Sambo Junaidu, ya fitar.

Shugaban kwamitin ya bayyana saƙon Sarkin kamar haka:

"Wannan sanarwar na umurtar ɗaukacin al'ummar musulmi cewa ranar litinin,12 ga watan Afrilu, 2021 wanda ya zo dai-dai da 29 ga watan Sha'ban, 1442AH, ita ce ranar da za'a fara neman jinjirin watan Rahamadana na shekarar 1442AH."

"Sabida haka ana umurtar musulmi da su fara neman jinjirin watan daga ranar Litinin kuma sukai rahoto idan sun ganshi."

"Ana umartar duk wnda ya ga watan da ya kai rahotonsa ga shugaban ƙauyensu don isar da saƙon ga fadar mai martaba Sarkin Musulmi"

Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin
Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin Hoto: Dailynigerian.com
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

Sarkin ya kuma yi addu'ar Allah ya taimaki musulmai gaba ɗaya wajen sauke nauyin da ya ɗora musu na yin azumin wata ɗaya (Ramadan).

Malam Junaidu ya kuma bada lambobin wayan da za'a kai rahoton ganin jinjirin watan kai tsaye zuwa ga kwamitiin kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Lambobin wayan sun haɗa da: 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 da kuma 08035945903.

A wani labarin kuma Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce Najeriya ba zata taɓa daina ciwo bashi daga waje ba musamman idan ya zama dole ba yadda zata iya saboda tana son cika kasafin kuɗi.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel