Yari: Gwamnan Zamfara zai yi asarar kujerarsa idan ya yi gangancin sauya-sheka zuwa APC

Yari: Gwamnan Zamfara zai yi asarar kujerarsa idan ya yi gangancin sauya-sheka zuwa APC

- Abulaziz Yari ya yi kira ga Bello Matawalle ya guji barin jam’iyyarsa ta PDP

- Tsohon Gwamnan ya ce Magajinsa zai rasa kujerarsa muddin ya sauya-sheka

- Yari ya ce kotu ta zartar da hukunci cewa PDP ce za ta rike Zamfara har 2023

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji AbulAziz Yari, ya bayyana cewa gwamna Bello Matawalle zai tashi a tutar babu idan har ya koma jam’iyyar APC.

Jaridar Punch ta rahoto Alhaji AbulAziz Yari ya na cewa Gwamna Bello Matawalle zai iya rasa kujerarsa, muddin ya sauya-sheka daga jam’iyyarsa ta PDP.

Babban jigon na APC, AbulAziz Yari ya bayyana cewa Bello Matawalle zai yi asarar kujerar gwamna idan aka yi la’akari da yadda ya samu mulki a 2019.

KU KARANTA: Matawalle ya yi taka-tsan-tsan da yadda yake mulki - Yari

Rahotanni sun bayyana cewa Yari ya yi wannan maganar ne a babban sakatariyar jam’iyyar APC da ke garin Gusau a ranar Lahadi, 11 ga watan Afrilu, 2021.

Tsohon gwamnan ya ziyarci ofishin APC ne domin ya yi rabon hatsin azumi na Naira miliyan 1.3 da ya saya domin a raba wa ‘ya ‘yan jam’iyya a jihar Zamfara.

A cewar Yari, babu wanda ya sanar da shi a takarda ko kuma da fatar baki cewa gwamna Matawalle ya na yunkurin fice wa daga PDP, ya shigo jam’iyyar APC.

Yari ya yi kira ga magajinsa ya yi hattara da barin jam’iyyar PDP domin hukuncin da kotun koli ta yi shi ne PDP ce za ta cigaba da mulki a jihar Zamfara har 2023.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnonin Kudu maso gabas sun kafa Jami’an Ebube Agu

Yari: Gwamnan Zamfara zai yi asarar kujerarsa idan ya yi gangancin sauya-sheka zuwa APC
AbulAziz Yari da Gwamna Bello Matawalle
Asali: UGC

“Har sai lokacin nan ya shude, duk wani ‘dan PDP da yake kan kujerar mulki da ya sauya-sheka, zai rasa kujerarsa, idan aka duba hukuncin kotu.” Inji Alhaji Yari.

A cewar tsohon gwamnan, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC su na tunzura gwamnan na Zamfara ya yi watsi da jam’iyyarsa, ya manta da yadda ya samu mulkin jihar.

Sanata Kabiru Marafa ne ya wakilci AbulAziz Yari a wajen rabon kayan azumin. Hakan ya nuna cewa jagororin na APC sun dinke barakar da ke tsakaninsu a baya.

Kwanakin baya kun ji cewa rade-radi sun yi karfi cewa gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya fara shirin komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Tun kafin yanzu akwai jita-jitar sauya shekar Bello Matawalle, wanda ya zama gwamna a Zamfara karkashin jam'iyyar PDP bayan hukuncin Kotun Koli a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel