Ba kungiyar IPOB bane ta kashe Hausawa 7 mahauta a Imo, in ji shugaban Hausawa a Imo

Ba kungiyar IPOB bane ta kashe Hausawa 7 mahauta a Imo, in ji shugaban Hausawa a Imo

- Wani shugaban Hausawa a jihar Imo ya karyata zargin da ake yiwa kungiyar IPOB da kisan Hausawa

- Ya siffanta kisan Hausawa mahautan 7 da rikicin siyasa da kuma shirin tunzura 'yan Arewa

- Hakazalika ya yi bayyana cewa 'yan siyasa ne ke rura wutar rikici don raba al'ummar Ibo da Hausawa

Mataimakin ko'odinetan al'ummar Hausawa a jihar Imo, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, wanda aka fi sani da Garkuwan Hausawa, ya yi magana a wata hira da jaridar Punch game da kisan wasu mahauta bakwai a jihar da wasu 'yan bindiga suka yi.

Sulaiman ya bayyana cewa, babu shakka kisan Hausawan bakwai wani yunkuri ne na ta da zaune tsaye, musamman ma fada ta kabilanci, yana mai nuna takaicin irin wannan aika-aikata tare da mika wuya ga kaddarar Allah.

Da aka tambayeshi dangane da abinda ya fahimta a matsayin dalilin da yasa 'yan bindigan suka kashe mahautan, Sulaiman ya ce:

"Kashe-kashen na da nasaba da siyasa. Ba shi da wata alaka da 'Yan asalin Biafra ko kungiyar tsaro ta Gabas.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya da dama sun makale a yayin da dutse ke aman wuta a Tsibirin Caribbean

Ba kungiyar IPOB bane ta kashe Hausawa mahauta a Imo, in ji shugaban Hausawa a Imo
Ba kungiyar IPOB bane ta kashe Hausawa mahauta a Imo, in ji shugaban Hausawa a Imo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

"'Yan siyasan da suka fusata, wadanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da ke faruwa a jihar Imo, su ne suka kitsa kashe-kashen.

"Suna son mayar da jihar Imo mara dadin mulki ga fitaccen sanata Hope Uzodinma, amma da yardar Allah, ba zasu taba yin nasara ba.

Ya kuma bayyana cewa, maharan sun afkwa al'ummar Hausawa ne saboda 'yan Arewa su tunzura su fara fada al'ummar Ibo da ke zaune a yankunan Arewa.

Sulaiman ya kuma wanke kungiyar IPOB da ake zargin su suka kai wa Hausawan hari, in da yake cewa,:

"Masu kisan suna kokarin nuna kamar kungiyar IPOB ce ta shirya kisan, amma ba IPOB ba ce; kashe-kashen na da alaka da siyasa. Wadanda suke yiwa Gwamnatin jihar Imo mummunan fata ne suka dauki nauyin wadanda suka yi kisan."

KU KARANTA: Jarumin Korona: Buhari ya taya Dangote murnar zagayowar ranar haihuwa

A wani labarin, Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ta kai wa al'ummar Hausawa da ke yankin Orlu a jihar ta Imo.

Lamarin dai ya jefa al'ummar Hausawan da ke yankin cikin zaman zulumi.

A cewar wani dan kasuwa Bahaushe mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya da suka tafka da haura ta kusan naira miliyan 42.

Asali: Legit.ng

Online view pixel