Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje

Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje

- Gwamnatin jihar Kano ta ce tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ya sauka ya bar musu bashi mai tarin yawa

- A cewar gwamnatin, ya bar kimanin bashin naira biliyan 54 na gyaran titunan da suke kananun hukumomi 44

- Kwamishinan labarai, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da manema labarai hakan a ranar Lahadi bayan fitowarsu daga wani taro

Gwamnatin jihar Kano ta ce tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso ya bar mata basuka na fiye da N54,000,000 na gyaran tituna masu 5KM a cikin kananun hukumomi 44 da suke cikin jihar.

Kwamishinan jihar na labarai, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da manema labarai hakan a ranar Lahadi bayan fitowarsu daga wani taro, The Punch ta ruwaito.

"Gwamnatin Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ta barmu da bashin N54,408,259,638.05 na gyaran titi mai tsayin 5km dake cikin kananun hukumomi 44 na jihar," kamar yadda ya bayyana.

KU KARANTA: OPC, IPOB da Boko Haram duk abu daya ne, babu banbanci, Dambazau

Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje
Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ganduje ne mataimakin gwamna kuma kwamishinan harkokin kananun hukumomi a lokacin mulkin gwamna Rabi'u Kwankwaso.

Kamar yadda takardar tazo, gwamnatin ta samu rahoto akan duba kwangilar tituna masu 5km wanda tsohuwar gwamnati ta bayar a karkashin ma'aikatar LPP da kuma UPDA wacce zata duba ayyukan.

"Kwamitin ta kai ziyara kananun hukumomi 38 inda ta samu rahotonni akan yadda aka bayar da kwangilar, kudin sallamar ma'aikata da kuma kudin da aka saki na ayyukan," kamar yadda takardar tazo.

Kwamishinan ya bayyana ayyukan tituna masu 5km din na kananun hukumomi uku wadanda aka amsa aka baiwa wasu saboda kin aiwatar dasu a Warawa, Ungogo da Dawakin Tofa.

Sai kuma kwangilolin Tsanyawa da Bichi da suke kan titin Kano zuwa Katsina da aka saki bisa amincewar babbar ma'aikatar ayyuka da gidaje wacce gwamnatin tarayya ta bukaci hakan.

Takardar ta bayyana yadda sauran kwangiloli 3 na Rimin Gado, Karaye da karamar hukumar Bunkure suka fada cikin wadanda aka kwace aka sake baiwa wasu, sai na cikin birnin kano na Dala, Nassarawa, Gwale, Municipal da Tarauni duk aka kirgasu a cikin kwangilolin 5km.

A cewar Garba, gwamnatin ta amince da sakin naira miliyan 607.1 na gyaran titunan Rimin Gado zuwa Sabon Fegi-Jilli-Gulu na Karamar hukumar Rimin Gado.

KU KARANTA: Yajin aiki: FG na zargin likitoci da wasa da rayukan 'yan Najeriya

A cewarsa an amince da bunkasa makarantar Unguwar zoma dake Gezawa zuwa matsayin makarantar koyon jinya ta Gezawa don samun ingantaccen ilimin unguwar zoma da kuma rage mutuwar jarirai a jihar.

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka wuraren Molai dake Maiduguri inda suka kashe sojoji 3 da yammacin Asabar kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar.

Akwai kuma fararen hula da suka kashe wadanda har yanzu ba a tabbatar da yawansu ba, bayan sun kai farmaki Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar dake jihar Borno.

Duk hare-haren nan sun faru ne bayan Gwamna Zulum ya bar jihar inda ya kai ziyara jami'ar jihar Ibadan wacce suka bashi lambar jinjina ta 'Tsohon dalibi mai tarin nasarori'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel