Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak

Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak

- 'Yan Boko haram sun lallaba wuraren Molai dake Maiduguri inda suka kashe wasu sojoji 3 da wasu da yammacin ranar Asabar

- Al'amarin ya faru ne a lokacin da Gwamna Zulum ya kai ziyara jami'ar jihar Ibadan don amsar jinjina da suka yi masa

- Ganau sun bayyana yadda 'yan ta'addan suka je suka yi kaca-kaca da kayan amfanin babban asibitin jihar

Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka wuraren Molai dake Maiduguri inda suka kashe sojoji 3 da yammacin Asabar kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar.

Akwai kuma fararen hula da suka kashe wadanda har yanzu ba a tabbatar da yawansu ba, bayan sun kai farmaki Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar dake jihar Borno.

Duk hare-haren nan sun faru ne bayan Gwamna Zulum ya bar jihar inda ya kai ziyara jami'ar jihar Ibadan wacce suka bashi lambar jinjina ta 'Tsohon dalibi mai tarin nasarori'.

Mazauna Damasak da harin bai kai musu ba sun tabbatar wa da Vanguard cewa maharan sun shiga babban asibiti ne inda suka sace kayan amfanin asibitin kuma suka lalata wasu.

KU KARANTA: Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar gwamnatin Buhari a wasu lokuta

Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak
Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An tura 'yan sanda tsaron yankunan Hausawa a Imo

Maharan sun sace wasu motocin asibitin da sauran ababen hawan ma'aikatan asibitin yayin da suka kona wasu.

Batun kashe sojoji 3, wata majiya ta bayyana yadda lamarin ya faru wuraren karfe 7 bayan 'yan bindigan sun sanya kayan sojoji suka ratsa Molai tare da budewa sojojin wuta.

Majiyoyin sun bayyana yadda mazauna yankin da jami'an tsaro suka yi ta tserewa da gudu don samun tsira kafin a tura 'yan sanda don su kwantar da tarzomar.

Shugaban karamar hukumar, Mustapha Bunu Kolo Mobbar, ya tabbatar da kashe-kashen da aka yi a Damasak inda yace lamarin ya matukar daga masa hankali.

"Tabbas, 'yan Boko Haram sun kai mummunan hari Damasak jiya da daddare.

"Abinda yafi tada hankalin kowa shine yadda suka kashe mutane 6 yayin da sojojin sama suke taimakon na kasa suka samu wani abin hawan 'yan Boko Haram da ya shiga wani gidan suna da jama'a suka taru.

"Sai da 'yan bindigan suka lalata duk wani abin amfani sannan suka kwashe kayan abinci a wata ma'adanar gwamnati.

"Sai da suka biya asibiti suka sace motoci da duk wasu abubuwan amfani na asibitin," cewar Kolo.

Shugaban karamar hukumar ya yabawa 'yan sa kai da mafarauta da suka mayar da harin baya da hakan da lamarin ya fi haka kazanta.

An yi kokarin tattaunawa da jami'in hulda da jama'an yankin, DSP Edet Okon amma hakan bai yuwu ba.

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace ba zai baiwa wani mai garkuwa da mutane ko sisi ba koda kuwa dansa ne yake hannunsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirar gidan rediyo da aka yi dashi ranar Juma'a akan yadda gwamnatinsa take bullo wa 'yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya dade yana bayyana yadda yake amfani da karfi wurin magance ta'addanci a jiharsa, kuma yana tsaye akan bakarsa. Ya maimaita a ranar Alhamis cewa babu wani dan ta'adda daya dace ya rayu a duniya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel