OPC, IPOB da Boko Haram duk abu daya ne, babu banbanci, Dambazau
- Tsohon shugaban sojin kasa ya kwatanta IPOB da OPC da kungiyar Boko Haram
- A cewarsa, kungiyoyin guda biyu suna yunkurin mayar da Najeriya filin daga
- Dambazau ya bayyana hakan ne a Abuja inda yace suna zakewa a lamurransu
Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban sojin kasa, ya kamanta kungiyoyin IPOB da OPC da kungiyar Boko Haram.
A cewarsa OPC da IPOB suna yunkurin tayar da tarzomar kabilanci a Najeriya. Ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma'a a Abuja, inda Dambazau ya bayyana kamanceceniyarsu da Boko Haram wacce ta fara a 2009.
Ya yi bayani akan yadda suke nuna zakewa da kuma kawo cikas.
"Ba jihohi suke yi wa yaki ba: suna da wata manufar ta daban ta raba kan al'ummar kasar Najeriya. Basu yarda da hadin kai ba kamar yadda Boko Haram take," a cewar Dambazau.
KU KARANTA: Bashir El-Rufai: A kan me 'yan arewa zasu bukaci lasisin tuki a kasar da take mallakinsu
"Kungiyoyin nan biyu suna iyakar kokarinsu wurin tayar da tarzomar kabilanci sakamakon yadda suke kai hare-hare ga 'yan arewa dake sana'o'insu a kudu don su janyo rabuwar kawuna.
"Hanyarsu daya da Boko Haram, duk masu zakewa ne a wurin amfani da sunan addini don su yi cuta."
Tsohon ministan cikin gidan ya shawarci 'yan sanda da su sanya ido kwarai don kwantar da hankula.
"Na yarda da cewa indai aka zage wurin dakatar da ta'addancinsu da rashin tsaro, za a cimma gaci," a cewarsa.
"Aikin 'yan sanda ne tabbatar da doka kuma wajibi ne 'yan sandanmu su motsa akan wannan al'amarin."
Dama TheCable ta ruwaito yadda IPOB ta jagoranci kashe 'yan arewa a kudu maso gabas a Najeriya.
KU KARANTA: Jiya ba yau ba: Tsoffin hotunan biloniyoyi Dangote, Adenuga da Otedola sun bada mamaki
A wani labari na daban, Aisha, matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana yadda take ji game da mulkin mijinta wanda take kalubalanta a wasu lokuta.
A littafin tarihinta da aka kaddamar a ranar Alhamis, uwargidan shugaban kasan tace tana caccakar gwamnatin ne saboda yadda take kaunar shugabanci nagari.
A littafinta, Aisha Buhari ta bayyana yadda aka aurar da ita a kananan shekaru da kuma martanin da tayi wa shugaban kasan a kan tsokacin da yayi na cewa madafi ne huruminta.
Asali: Legit.ng