Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata

- Rikici ya barke a gidan yarin jihar Bauchi biyo bayan wata husuma tsakanin jami'i da fursunoni

- An kame wani jami'i dake kawo wa fursunoni miyagun kwayoyi da wayoyin salula gidan yari

- An ruwaito cewa, fursunonin sun afkawa wani shago tare da daukar adda, cebur da matoni

Wani rikici da ya barke a Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya dake Bauchi, ya bar fursunoni biyar da jami’ai biyu cikin rauni, a cewar mai magana da yawun cibiyar, Mista Abubakar Adamu, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Juma’a, a Bauchi cewa lamarin ya faru ne sakamakon fataucin kayayyaki ga fursunoni da wani jami’in gidan yarin ke yi.

“Wani rikici da ya barke sakamakon wani jami’in gidan yari da ke fataucin wayoyin salula, kwayoyi da sauran abubuwa masu nasaba, ga fursunoni da ke cikin cibiyar.

“Abin takaici ga jami’in, jami'an sirri sun kama shi yayin gudanar da bincike, fursunonin sun samu labarin abin da ya faru suka kutsa kai cikin shagon suka kwashe cebur, adda da kuma matoni.

KU KARANTA: Duk da batan jirgin sojin sama, sojoji sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata
Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata Hoto: lailasnews.com
Asali: UGC

“Fursunonin, wadanda ke rera wakoki, sun fasa wasu kayayyaki a cikin gidan yarin wanda hakan ya tilasta jami’an gidan yarin suka fara harbin iska don tsoratar da su. A cikin rikicin, fursunoni biyar da jami’ai biyu sun ji rauni,” inji shi.

Mista Adamu ya ce an shawo kan lamarin, yayin da fursunonin suka koma dakunansu, ya kara da cewa yakamata jama'a su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tunda kwanciyar hankali ya dawo cibiyar.

NAN ta ruwaito cewa an tsaurara matakan tsaro, tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa da zirga-zirga a yankin sannan an toshe hanyoyin da ke zuwa cibiyar gyara.

KU KARANTA: Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga sun saki akalla fursunoni 2,000 a hedikwatar Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya (NCS) dake Owerri a Jihar Imo.

'Yan bindigan sun kuma kai hari ofishin da ke kusa da sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) na rundunar 'yan sandan jihar, tare da sakin wadanda ake zargi a wurin.

Maharan sun kona kusan dukkan motocin da ke ajiye a hedikwatar sannan kuma suka kubutar da dukkan wadanda ake zargi a kusan dukkanin sassan da ke SCID din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel