Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan

Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan

- Karamin ministan albarkatun man fetur ya bayyana irin kaunar da Buhari ke yiwa yankin Neja Delta

- Ministan ya bayyana soyayyar Buhari ga mutanen yankin cewa na da nasaba da Goodluck Jonathan

- Ya kuma bayyana cewa, Buhari na sane da kokarin samarwa matasan yankin ayyukan yi

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana kaunar mutanen Ogbia, wata karamar kabilar Ijaw a cikin jihar Bayelsa.

Ministan ya ce dalili kuwa daya ne, saboda dansu, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya bar masa mulki cikin lumana a 2015, The Nation ta ruwaito.

Sylva ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya ke duba aikin da ake yi na samar da Man Fetur da Gas na Kasa (NOGaPS) wanda Hukumar NCDMB ke ginawa a Emeyal 1, karamar hukumar Ogbia ta jihar.

K KARANTA: Duk da batan jirgin sojin sama, sojoji sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP

Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan
Hoto: thebreakingtimes.com
Minista ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke matukar kaunar kabilar su Jonathan
Asali: UGC

Sylva, wanda tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya ce: “Shugaba Muhammadu Buhari musamman yana son mutanen Ogbia kuma zan iya fada muku karara.

"Buhari yana kaunar mutanen Ogbia saboda Goodluck Jonathan, wanda ya kasance Shugaban Tarayyar Najeriya, da yardar ransa ya yarda da sauyin da aka samu cikin kwanciyar hankali a Najeriya.

"Don haka, kuna iya ganin cewa daya daga cikin hanyoyin da Shugaban kasa yake ginawa a Najeriya, hanyar Sukuk, tana cikin yankin Ogbia ne, wanda ke kaiwa ga jama'ar Goodluck Jonathan."

Sylva ya yaba wa matasan Ogbia saboda kasancewa cikin lumana kuma ya bukace su da su kasance masu dabi’ar, ya kara da cewa za su cimma nasarori da yawa saboda zama lafiya.

Da yake bayyana mataki da ingancin aikin da aka yi a yanzu na NOGaPS a matsayin mai gamsarwa, Ministan ya ce idan aka kammala, aikin zai samar da ayyuka sama da 2,000.

Ya lura cewa Buhari na sane da cewa samar da ayyukan yi ne kawai zai iya magance matsalolin yankin Neja Delta mai arzikin mai.

KU KARANTA: Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littafin Aisha Buhari

A wani labarin, A ranar Talata ne kungiyar kiristocin Najeriya ta yi wa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), caa, tare da bayyana shi a matsayin wanda bai cancanta ba, jaridar Punch ta ruwaito.

Kungiyar ta CAN ta kuma bayyana gwamnatin mai ci ta Buhari a matsayin mai nuna wariyar addini.

Shugaban kungiyar, Samson Ayokunle, ya fadi hakan ne a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yayin da yake jawabi a wurin taron Holy Convocation da cocin Victory Life Bible Church ya shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel