Hankali ya tashi yayin da wasu da ake zargi 'yan fashi ne suka yi ruwan harsasai a kan sarkin Ekiti
- Elewu na Ewu Ekiti, Oba Adetutu Ajayi ya tsallake rijiya da baya
- Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai wa basaraken hari a kan babbar hanya
- ‘Yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan al'amarin
Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a jihar Ekiti sun bude wuta a kan motar Elewu na Ewu Ekiti, Oba Adetutu Ajayi, inda suka ji wa basaraken rauni a yayin harin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun kaiwa basaraken hari ne da yammacin ranar Juma’a, 9 ga Afrilu, lokacin da yake tafiya a cikin motarsa ta aiki zuwa Ayetoro da ke makwabtaka a Ekiti.
KU KARANTA KUMA: An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta
Wata majiya ta ce basaraken ya samu raunin harbin bindiga kuma yanzu haka ana kula da shi a wani asibiti da ba a bayyana ba a jihar ta Ekiti.
A cewar majiyar:
“Basaraken yana tafiya a motarsa zuwa Ayetoro lokacin da‘ yan fashin suka far masa kuma a kokarin tserewa, suka bi shi sannan suka yi ruwan bindiga a motarsa.
“Harsasai sun same shi a kafafuwa, hannaye da kuma ciki. Yanzu haka basaraken yana kwance a wani babban asibitin garin Ekiti."
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Ekiti ta tabbatar da harin da aka kaiwa sarkin.
KU KARANTA KUMA: PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal
Sunday Abutu, mai magana da yawun rundunar yace kwamishanan ‘yan sanda na Ekiti ya yi alkawarin cewa za a hukunta wadanda suka kai harin.
A wani labarin, mai martaba Sarkin Lere, Birgediya Janar Abubakar Garba Mohammed (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 77 a duniya.
Wata majiya daga garin na Lere da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa Legit.ng Hausa rasuwar sarkin.
Marigayi Abubakar Garba ya taba gwamnan jihar Sokoto a karkashin gwamnatin mulkin soja na Badamasi Babangida.
Asali: Legit.ng