Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi

Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi

- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ganin yan bindiga ya fi ganin Buhari sauƙi

- Dr Hakeem Baba Ahmed, Kakakin kungiyar dattawan arewa ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a Twitter

- A cewar Baba Ahmed, Gumi ya ce ya shafe watanni yana ganawa da ƴan bindiga amma kuma ya yi watanni yana ƙoƙarin ganin Buhari abin bai yiwu ba

Sheikh Ahmad Gumi, babban malamin addinin musulunci mazaunin jihar Kaduna ya ce ganin ƴan bindiga ya fi ganin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cewar Dr Hakeem Baba Ahmed, kakakin kungiyar dattawan arewa, Gumi ya faɗawa masu ruwa da tsaki a yankin cewa ya daɗe yana ƙoƙarin ganin Buhari kan batun tabarɓarewar tsaro amma hakan bai yi wu ba.

Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi
Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa

Malamin addinin ya ziyarce dazuka daban-daban domin tattaunawa da ƴan bindigan da nufin kawo karshen hare-haren da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

"Yau, Sheikh Dr Abubakar Gumi ya shaidawa mutanen wurin taro a Kaduna yadda shafe watanni yana ganawa da yan bindiga, da kuma karin wasu watannin yana ƙoƙarin ganawa da shugaban kasa domin ya bashi shawara kan yadda za a magance matsalar. Ya ce ganin yan bindiga ya fi ganin shugaban ƙasa sauƙin," kamar yadda Baba Ahmed ya wallafa a Twitter.

Rubutun da Baba Ahmed ya wallafa a Twitter ya janyo cece-kuce amma kakakin na kungiyar arewa ya kare abin da ya rubuta.

"An riga an san matsayar Gumi a kan ƴan bindiga. Dole ne sai ya gana da shugaban kasa gaba-da-gaba kafin ya bashi shawara?" @Vincentita1 ya rubuta.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro

Baba Ahmed ya bashi amsa kamar haka, "Ta yaya zan yi jayayya da wanda ya fi ni sanin harkokin tsaro ko yadda za a magance su? Abin da na sani shine Gumi tsohon Kwanel ne a rundunar soja kuma akwai yiwuwar ya gano wasu abubuwa da za su yi amfani idan ya faɗa wa shugaban kasa gaba-da-gaba. Mai na sani?"

Mustapha Hadi ya yi tambaya, "Shin Gumi bai zai iya bawa Ministan tsaro shawararin ba?"

Baba Ahmed ya mayar da martani, "Ministan tsaro yana karkashin shugaban kasa ne, don haka shugaban kasa ne ke ɗaukan matakin karshe kan batutuwan tsaro."

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel