Dattawan Arewa sun yanke hukunci: Sun amince da tsarin shugabancin karba karba

Dattawan Arewa sun yanke hukunci: Sun amince da tsarin shugabancin karba karba

- Kungiyoyin zamantakewar siyasa na Arewa sun cimma matsaya kan sake fasalin kasar

- Kungiyoyin sun yi amannar cewa sake fasalin zai amfani Najeriya

- Yankin arewa ya taba adawa da kiran da ake na sake fasalin lamuran kasar

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da sauran shugabannin yankin sun bayyana cewa ba za a shafa wa yankin bakin fenti ba wajen daukar manyan shawarwari game da shugabancin karba-karba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyoyin sun yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a, 9 ga Afrilu, bayan taron kwanaki biyu a Arewa House Kaduna.

KU KARANTA KUMA: An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta

Dattawan Arewa sun yanke hukunci: Sun amince da tsarin shugabancin karba karba
Dattawan Arewa sun yanke hukunci: Sun amince da tsarin shugabancin karba karba Hoto: Northern Elders Forum (NEF)
Asali: Facebook

Kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Coalition of Northern Groups (CNG) Arewa Consultative Forum (ACF) da sauransu.

Kungiyoyin sun bayyana sake fasalin kasar a matsayin abu mai mahimmanci ga ci gaban Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa daya.

A cewar jaridar The Guardian, sun lura cewa arewa zata fi karfi idan ta magance gazawar ta na ciki.

Kungiyoyin sun ce: Don rayar da Najeriya, dole ne dukkan bangarorin kasar su dukufa wajen tallafawa ci gabanta a matsayin abu daya, ba tare da sanya wani takamaiman sharadi ba.

KU KARANTA KUMA: PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

A baya mun ji cewa Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya bayyana cewa arewa ba za ta yi amfani da kabila da addini ba wajen zaben shugabanni a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yace ‘yan arewa sun koyi darasi mai tsadar gaske.

Legit.ng ta tattaro cewa Abdullahi ya bayyana cewa babu wani dan arewa da za a ba tabbacin samun goyon bayan yan arewa don kawai ya kasance dan yankinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel