A nuna mana gawawwakinsu: Soja ya karyata ikirarin cewa an kashe mutum 70 a Binuwai
- Wani jami'in soja ya musanta ikirarin cewa sojoji sun kashe mutane 70 da basu jiba basu gani ba a jihar Binuwai
- Ya kalubalanci mazauna yankin da suka yi wannan ikirari da su nuna gawawwaki ko kaburburan da aka binne mutanen don tabbatar da zarginsu
- Sojan ya jaddada cewa baya ga mutum shida da aka harbe bayan samunsu da bindigogin sojojin da aka kashe babu wani da aka halaka
Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wani soja ya karyata ikirarin cewa sojoji sun kashe sama da mutane 70 a jihar Binuwai.
A wani taron manema labarai a ranar Juma’a, mutanen Mbator a Shangev-Tiev na Karamar Hukumar Konshisha da ke Jihar Benuwai, sun ce yayin da aka kashe sama da mutane 70 da ba su ji ba ba su gani ba, 100 sun bata yayin luguden wuta da sojoji suka yi ta sama da kasa.
Mazauna garin sun roki Gwamnatin Tarayya da ta umarci sojoji a kan su dakatar da kashe-kashen, suna masu cewa suna shirin afkawa karin kauyuka.
KU KARANTA KUMA: Buhari yayi sharhi akan batutuwan da suke hana matarsa bacci
Jaridar ta ruwaito yadda sojoji suka mamaye garin bayan an kashe sojoji 11 a wani kwanton bauna.
Da aka tuntube shi don ya yi tsokaci game da zargin na mazauna kauyen, Manjo Janar Adeyemi Yekini, kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), ya tura wakilin jaridar zuwa sashin yada labarai na Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.
Amma wani soja, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi watsi da iƙirarin na mazauna ƙauyen, yana ƙalubalantar su da tabbatar da wannan ikirari nasu.
Ya bayyana cewa sojojin da aka kashe dakarun bataliya 72, runduna ta musamman na sojin Najeriya ne.
Sojan ya ce baya ga mayaka 12 da aka “kashe a ranar Laraba, babu wani mutum da aka kashe.”
Ya ce an kwato bindigogin sojojin da suka mutu daga hannun miyagun da aka kashe.
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari: Rayuwar da na yi a gidan shugaba Buhari tun ina da shekaru 18
“Wadanda ke ikirarin cewa sojoji sun kasha mutane 70 su tabbatar da hakan da gawarwaki ko kuma su nuna mana kaburburan da aka binne su. Ina gawawwakin suke? ”
Gwamna Samuel Ortom ya bukaci mazauna kauyen da suka kwace makaman sojojin da su dawo dasu.
A baya mun ji cewa Mutanen Mbator a Shangev-Tiev na karamar hukumar Konshisha da ke jihar Benuwe a ranar Juma’a, sun yi ikirarin cewa akalla bayin Allah da basu ji ba basu gani ba guda 70 aka kashe a mamayar da sojoji suka kai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kauyukan Bonta na Mbator a Shangev-Tiev na karamar hukumar Konshisha da Okpute-Ainu a karamar hukumar Oju sun kwashe tsawon shekaru da dama suna rikici kan filaye wanda hakan ke sa a tura jami'an tsaro don kwantar da rikicin.
Sabon rikici ya ɓarke a tsakanin garuruwan biyu kwanaki biyar da suka gabata kuma wannan ya yi sanadiyar tura sojoji.
Asali: Legit.ng