CAN ta caccaki Buhari: Ba a zabe ka don kazo ka yi korafi kan shugabancin baya ba
- Kungiyar kiristocin Najeriya ta caccaki shugaba Buhari kan lamarin rashin tsaron kasar
- Kungiyar ta ce 'yan Najeriya ba su zabi shugaban ba don yake korafin shugabannin baya
- Kungiyar ta kuma koka kan yadda masu aikata laifi suka fi jami'an tsaro nuna kwarewa
A ranar Talata ne kungiyar kiristocin Najeriya ta yi wa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), caa, tare da bayyana shi a matsayin wanda bai cancanta ba, jaridar Punch ta ruwaito.
Kungiyar ta CAN ta kuma bayyana gwamnatin mai ci ta Buhari a matsayin mai nuna wariyar addini.
Shugaban kungiyar, Samson Ayokunle, ya fadi hakan ne a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yayin da yake jawabi a wurin taron Holy Convocation da cocin Victory Life Bible Church ya shirya.
KU KARANTA: An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai
Ayokunle, wanda ya yi magana a taron mai taken, ‘Yanayin kasar nan: Hanyar da za a bi a samu mafita’, ya bayar da hujjar cewa rashin tsaro da sauran munanan halayen da ake gani a kasar nan sakamakon sakaci ne daga bangaren gwamnatin Buhari.
Ayokunle, wanda shi ma ya nuna damuwarsa da yawaitar rashin tsaro da aikata laifuka a kasar, ya koka kan yadda masu aikata laifuka suka fi nuna kwarewa fiye da jami'an tsaro a Najeriya.
Ya ce game da Shugaban kasar, “Mun zabe ka ne don kare kasar; ba mu sanya ka can don kana gunaguni game da shugabanni marasa nagarta ba.
“Masu aikata laifi sun fi nuna kwarewa fiye da yadda jami’an tsaro ke yi a lokuta da dama.
"Kana korafi game da shugabannin da suka shude; mun san cewa shugabannin da suka shude ba su yi abin kirki ba kuma mun zabe ka ne don kawo canji."
KU KARANTA: Yajin aiki: Minista Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa
A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wani fitaccen malamin addini a Arewa, Sheikh Ahmad Gumi, sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.
Obasanjo da Gumi sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanya hannu bayan sun yi wata ganawar sirri a dakin karatun Obasanjo dake Abeokuta a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.
A wani bagnaren sanarwar, ance; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yankin.
Asali: Legit.ng