'Yan sanda sun ci Farai minista tara saboda karya dokar annobar korona

'Yan sanda sun ci Farai minista tara saboda karya dokar annobar korona

- 'Yan sanda a kasar Norway sun ci tarar Farai minista Erna Solberg saboda saba dokar COVID-19

- Solberg ta yi taro ne inda mutum 13 suka hallarci bikin cikarta shekaru 60 wadda hakan ya saba wa dokar bada tazara

- Shugaban yan sanda, Solberg, ya ce an ci Farai ministan tarar $2,352 kuma daga bisani ta nemi afuwar yan kasar

Rundunar yan sandan kasar Norway, a ranar Juma'a ta ce ta ci Farai minista Erna Solberg tara saboda karya dokar bada tazara na COVID-19.

An ci tarar Solberg ne bayan ta yi taron bikin zagayowar ranar haihuwarta da iyalanta suka hallarta kamar yadda reuters ta ruwaito.

'Yan sanda sun ci Farai minista tara saboda karya dokar annobar korona
'Yan sanda sun ci Farai minista tara saboda karya dokar annobar korona. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUB WANNAN: Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu

An ci ta tarar Norwegian crowns 20,000 ($2,352) a cewar shugaban yan sanda, Ole Saeverud kamar yadda ya fada yayin taron manema labarai.

Ministan ta nemi afuwa bisa shirya taron na murnar cikarta shekaru 60 inda iyalanta 13 suka hallarta a watan Fabrairu duk da cewa gwamnati ta saka doka kada mutum fiye da 10 su yi taro.

Duk da cewa ita da mijinta Sindre Finnes ne suka shirya taron, shi ba a ci shi tara ba.

An kuma samu wurin cin abincin da aka yi taron da laifi amma ba a ci shi tara ba shima.

KU KARANTA: Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30

"Solberg ce jagorar kasar kuma ta kasance kan gaba wurin umurtar mutane su bi dokoki domin dakile yaduwar cutar," in ji Saeverud.

A halin yanzu ofishin Farai ministan bai yi tsokaci kan batun ba.

An samu hauhawar wadanda ke kamuwa da kwayar cutar ta COVID-19 a farkon watannin shekarar 2021 hakan ya tilastawa gwamnatin tsaurara dokoki.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Source: Legit

Online view pixel