Rundunar 'Yan Sandan Nigeria ta bawa Sarkin Bauchi lambar yabo

Rundunar 'Yan Sandan Nigeria ta bawa Sarkin Bauchi lambar yabo

- Rundunar yan sanda ta bawa mai martaba sarkin Bauchi lambar yabo na zaman lafiya

- Sylvester Abiodun Alabi, kwamishinan yan sandan jihar ne ya mika wa Mai martaba Dr Rilwanu Sulaiman Adamu lambar yabon

- Kwamishinan yan sandan ya ce rundunar ta karrama sarkin ne saboda jajircewarsa wurin ganin an samar da zaman lafiya a jihar

Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Bauchi ta karrama Mai martaba sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu, saboda asassa zaman lafiya tsakanin mutane a masarautarsa da jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, Sylvester Abiodun Alabi, wanda ya mika lambar yabon ga sarkin a fadarsa, ya bayyana shi a matsayin mutum mai hada kan al'umma wanda ke jagorancin ganin an samu zaman lafiya a Bauchi.

Rundunar 'Yan Sandan Nigeria ta karrama Sarkin Bauchi da lambar yabo
Rundunar 'Yan Sandan Nigeria ta karrama Sarkin Bauchi da lambar yabo. Hoto: BBC/Leadership.ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu

Kwamishinan ya bawa sarkin tabbacin cewa rundunar za ta cigaba da yin ayyukanta na samar da tsaro ga al'umma da kiyayye dukiyoyinsu game da tabbatar da bin doka da oda.

Ya yi kira ga mazauna jihar su yi koyi da halayen sarkin sannan su cigaba da aiki da yan sanda wurin taimaka musu da bayanai kan wadanda ba su gamsu da su ba domin a tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A jawabinsa, mai martaba sarkin Bauchi, Dr Rilwan Sulaiman ya bukaci sabon kwamishinan yan sandan ya zama mai adalci wurin yin ayyukansa.

KU KARANTA: Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30

Ya kuma bukaci mutanen jihar su cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kai domin gudanar da ayyukansu na tsare rayyuka da dukiyoyin mutane.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel