Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu

Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu

Mata na kara nuna bajintarsu a duniya inda a wasu wuraren suke gogayya da maza wurin wasu ayyuka da sana'o'i da a baya ba haka lamarin ya ke ba. Bakwai daga cikin wadannan matan sune suka fi sauran arziki a duniya.

Kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, wadannan sune mata bakwai da suka fi arziki a duniya.

1. Francoise Bettencourt Meyers da Iyalanta

Francoise Bettencourt Meyers itace mace mafi arziki a duniya, an kiyasta arzikinta ya kai $73.6 biliyan (29,089,375,000,000). Ta gaji arzikin ne daga mahaifiyarta, Liliane Bettencourt wacce ta rasu a 2017.

Mahaifin Liliane ne ya kafa kamfanin kayan shafe-shafe na L'Oreal, inda Francoise ta yi aiki a nan tun 1997. A yanzu shekarunta 67.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Martin Bureau/AFP
Source: Getty Images

2. Alice Walton

Dukiyar Alice Walton, yar Amurka, mai shekaru 71, ya kai $61.8 biliyan (N23,561,250,000,000) hakan yasa itace mace ta biyu mafi dukiya a duniya. Ta samu dukiyarta ne daga manyan kantina na Walmart.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Rick T. Wilking
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

3. MacKenzie Scott

Dukiyar tsohuwar matar Jeff Bezo's ya kai $53 biliyan (N20,206,250,000,000). Ta samu dukiyarta ne daga kamfanin Amazon. Aurenta da Bezos ya zo karshe a 2019, wadda hakan yasa ta shiga jerin biloniyoyi a duniya.

Shekarunta 53 kuma yar kasar Amurka ce.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Jörg Carstensen/picture alliance
Source: Getty Images

4. Julia Koch da Iyalanta

Dukiyar Julia Koch ya kai $46.4 biliyan (17,690,000,000,000). Ita da 'ya'yanta sun mallaki kashi 40 cikin 100 na kamfanin Koch industries.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Neilson Barnard
Source: Getty Images

5. Miriam Adelson

Miriam Adelson ce mace ta biyar mafi dukiya a duniya, dukiyarta ya kai $38.2 biliyan (N14,563,750,000,000).

Shekarunta 75 a duniya, ita ce ta mallaki kashi 56 cikin 100 na gidan wasanni na Cas*no a Las Vegas.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Michael Tullberg
Source: Getty Images

6. Jacqueline Mars

Jacqueline Mars ta mallaki $31.3 biliyan (N11,933,125,000,000). Ta samu dukiyarta ne daga kamfanin Mars Incorporated, kamfani mai yin alawa da abinci da abincin dabobi.

Shekarunta 81 kuma yar kasar Amurka ce.

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Jay Mallin/Bloomberg
Source: Getty Images

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare ayarin motoccin sojoji, sun ƙwace N28m da makamai a Benue

7. Yang Huiyan da iyalanta

Yang Huiyan, yar kasar China mai shekaru 39 itace ke da kashi 58 cikin 100 na kamfanin dillancin gidaje na Country Garden Holdings.

Dukiyarta ya kai $29.6 biliyan (N11,285,000,000,000).

Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021
Jerin hamshakan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021. Photo credit: Yang Huiyan Foundation
Source: Facebook

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel