Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama

Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama

- Bayan ya kwana a Bama, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya rabawa 'yan gudun hijira N200,000,000 da kayan abinci

- Sai da ya tsaya tsayin daka ya tabbatar 'yan gudun hijira 70,000 sun amfana da wannan romon demokradiyyar a ranar Laraba

- 'Yan gudun hijiran sun dakata daga zuwa gonakinsu, kasuwanni da sauran wurare, shiyasa Zulum yayi wannan yunkurin

Gwamnan jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ya kwana yana rabawa 'yan gudun hijura 70,000 Naira miliyan 200 da kayan abinci a ranar Laraba, kuma sai da ya tsaya ya tabbatar kowannensu ya samu.

Dama an dakatar dasu daga zuwa kasuwanni, gonaki da sauran wuraren neman kudi sakamakon rashin tsaron daya addabi jihar. Sakamakon haka ne Zulum ya fara harkokin taimako da tallafawa a garesu. Ya jajirce kwarai wurin ganin ya samar da walwala da tsaro ga duk 'yan gudun hijira.

Wannan salon raba kudade da kayan abinci ya faru ne a wurare 5 dake garin Bama. Kowacce cikin shugabanni mata 40,000 ta samu fakitin suga guda biyu da kudi N5,000, wanda idan aka kirga sun kai N200,000,000.

KU KARANTA: Saurayi ya gwangwaje budurwar da N24m ranar zagayowar haihuwarta, 'yan mata sun gigice

Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama
Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama. Hoto daga The Governor of Borno
Source: Facebook

Shugabannin gidajen guda 30,000 sun samu buhun shinkafa, buhun masara da kwalin taliya.

"Muna sane da irin radadi da takaicin da kowannenku yake fuskanta kuma muna cikin damuwa kuma muna addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu" a cewar Zulum.

Gwamnan ya bayyana gyare-gyaren gidaje da 'yan Boko Haram suka lalata guda 1000 da yayi don masu gudun hijira su samu su koma.

Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama
Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama. Hoto daga The Governor of Borno
Source: Facebook

Zulum ya je fadar Shehun Bama, Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi, inda ya sanar da basaraken cewa yaje garin ne don gyaran makarantu kuma ya yi alkawarin taimakon yaran jihar Borno a bangaren ilimi.

Gwamnan ya amince da bukatar Shehun Bama akan cigaba da tallafa wa manoma don samun damar noma tunda damuna tana karatowa.

KU KARANTA: Matashin da ya aura mata 2 a rana daya ya bada labarin romon amarcin da yake kwasa

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bada umarni ga jami'ai da kada su tausayawa masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB), jaridar The Nation ta ruwaito.

Sifeta janar na 'yan sandan ya bada wannan umarnin ne yayin da ya ziyarci hedkwatar hukumar 'yan sandan Imo da aka kona da kuma gidan gyaran hali na Owerri a ranar Talata.

Adamu ya sanar da cewa dole ne 'yan sanda su yi amfani da makamansu wurin mitsike duk wani mai tada kayar baya.

Source: Legit.ng

Online view pixel