IGP: Nadin da Shugaban kasa Buhari ya yi ya saba dokar kasa da tsarin mulki inji fitaccen Lauya
- Mike Ozekhome ya soki nadin sabon shugaba Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya
- Lauyan da ke kare hakkin Bil Adama ya ce nadin ya saba tsarin mulkin kasa
- Ozekhome ya zargi Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke fifita ‘Yan Arewa
Lauya mai kare hakkin Bil Adama, Mike Ozekhome (SAN), ya bayyana nadin sabon shugaban ‘yan sanda na kasa a matsayin abin da ya saba doka.
Jaridar Punch ta rahoto Mike Ozekhome ya na cewa akwai kama-karya da keta doka a nadin da shugaban kasar ya yi a ranar 6 ga watan Afrilu, 2021.
Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sabon sufetan ‘yan sanda na kasa, Ozekhome ya fito ya soki wannan nadi.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin IGP a ofis
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ozekhome ya fitar da jawabi inda ya zargi shugaban Najeriya da Arewantar da gidan ‘yan sanda.
“Yau sai ga Buhari ya saka nada DIG U.A Baba, musulmin Arewa a matsayin mukaddashin IGP, yam aye gurbin wani musulmin Arewan, M.A Adamu.”
“Yayin da wani Musulmin Arewan, Alhaji Maigari Dingyadi, yake kujerar Ministan harkokin ‘yan sanda, an cike da’irar gidan ‘yan sanda da 'Yan Arewa.”
Lauyan ya cigaba da babatu ya na cewa: “Shin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya yin nadi a wajen addininsa ko a wajen bangaren da ya fito ba?”
KU KARANTA: Buhari ya nuna kiyayyar sa ga kabilar Igbo - Ozekhome
Wannan lauya ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta na nuna son kai, kabilanci, da yi da ‘yan gida.
Mista Ozekhome ya ke mamakin yadda shugaban kasar ya gaza samun wani jami’in tsaro daga wajen Arewa cikin tulin da ake da su da zai ba mukamin IGP.
Kafin yanzu, babban lauyan ya soki matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na kara wa’adin IGP M.A Adamu bayan lokacin ritayarsa ya yi.
A cewar Ozekhome SAN, shugaban kasa bai da ikon da zai nada shugaban ‘yan sanda shi kadai ba tare da ya tuntubi wadanda doka ta daura wa nauyi ba.
Lauyan yake cewa wadanda doka ta ba hurumin tabbatar da sabon IGP su ne majalisar ‘yan sanda wanda ya kunshi gwamnoni da shugaban hukumar PSC.
Asali: Legit.ng