Labari da duminsa: Ana harbe-harbe da bindiga a kusa da ofishin 'Yan Sanda a Aba

Labari da duminsa: Ana harbe-harbe da bindiga a kusa da ofishin 'Yan Sanda a Aba

- Mutane suna zaman dar-dar a garin Aba na jihar Abia bayan jin harbe-harben bindiga kusa da ofishin yan sanda

- Jami'an yan sandan sun rufe dukkan hanyoyin da suka bulle zuwa ofishinsu inda suka ce mutane su koma gida

- Majiya daga yan sandan ta ce sun samu bayannan sirri ne kan cewa yan bindiga na shirin kawo musu hari

A halin yanzu mutane na zaman dar-dar sakamakon jin karar harbe-harben bindiga a garin Aba da ke jihar Abia a kusa da inda ofishin yan sanda ya ke.

Mazauna garin suna gudanar da harkokinsu da suka saba kwatsam sai jami'an tsaro suka fara harbe-harbe da bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Labari da duminsa: Ana harbe-harbe da bindiga a kusa da ofishin Yan Sanda a Aba
Labari da duminsa: Ana harbe-harbe da bindiga a kusa da ofishin Yan Sanda a Aba
Asali: Original

An rufe dukkan hanyoyin da za su bulla da mutane zuwa unguwar da ofishin yan sandan ya ke an kuma umurci mutane su koma gidajensu.

Wani babban majiya daga rundunar yan sanda ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa jami'an sun samu bayanan sirri da ke nuna yan bindiga suna kan hanyarsu na zuwa Aba bayan kai hari ofishin yan sanda da ke jihar Imo.

KU KARANTA: Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

Yan bindiga sun rika kai hari a wurare daban-daban a Imo cikin wannan makon.

An saki fiye da fursunoni 1,800 a yayin da yan bindiga suka afka hedkwatar hukumar kula da gidajen gyaran hali na jihar.

An kuma kona motocci an saki wadanda ake tsare da su a yayin da yan bindigan suka afka hedkwatar yan sanda a Imo.

Rundunar yan sanda ta ce yan kungiyar IPOB masu fafutikan kafa kasar Biafra ne suka kai harin duk da cewa kungiyar ta musanta hakan.

Bayan saka wa sabon babban sufetan yan sandan Nigeria, Usman Alkali Baba baji a fadar shugaban kasa a Abuja, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce rundunar za ta sake tsari domin magance kallubalen tsaro a kasar.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel