Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes

Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes

- Forbes ta saki sunayen biloniyoyi na wannan shekarar inda mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ne na farko a jerin sunayen

- Shekara ta hudu kenan da yake kasancewa na farko kuma a kowacce shekara dukiyarsa habaka take yi sosai

- Kamar yadda attajirin mai shekaru 57 ya shaida, dukiyarsa ta kai dala biliyan 177 fiye inda ta karu fiye da shekarar data gabata

Forbes sun saki jerin sunayen biloniyoyin duniya na shekarar nan, kuma mai Amazon, Jeff Bezos ne ya kasance na daya a jerin, wanda shine a wannan matsayin na shekaru 4 kenan.

Dukiyar attajirin mai shekaru 57 ta kai dala biliyan 177 inda ta karu da dala biliyan 64 a shekarar data gabata sakamakon bunkasa hannayen jarin Amazon, kamar yadda jaridar ta tabbatar a ranar Talata, 6 ga watan Afirilu.

Mai kamfanin Tesla, Elon Musk ne wanda yafi kowa samun riba kuma ya kasance na biyu a jerin, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan 151, wanda ya karu da dala biliyan 24.6 a shekarar data gabata lokacin da ya kasance na 31 a jerin lokacin kimar dukiyarsa ta kai dala biliyan 24.6.

KU KARANTA: Matashin da ya aura mata 2 a rana daya ya bada labarin romon amarcin da yake kwasa

Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes
Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa

Idan aka hada dukiyar biloniyoyin sun zama dala tiriliyan 13.1, maimakon dala tiriliyan 8 na shekarar data gabata, a cewar Fobes.

"Masu arziki sun kara samun wasu tarin dukiyoyi masu yawa," cewar CCO Randall Lane a wata tattaunawa ta bidiyo da yayi da Reuters News.

A wannan shekarar an samu sababbin masu dukiya guda 493, ciki har da Whitney Wolfe Herd.

Duba jerin sunaye, tushen dukiya da kuma inda manyan biloniyoyin duniya 10 suke zama:

1. Jeff Bezos: Ya fi kowa arziki a duniya domin ya mallaki dukiyar da ta kai $177 biliyan kuma Amazon ne tushen dukiyarsa. Yana zaune ne a Seattle.

2. Elon Musk: Mashahurin mai kudin nan ya mallaki $150 biliyan kuma Tesla ne tushen arzikinsa. Mazaunin Austin ne dake Texas.

3. Bernard Arnault: Dukiyar wannan mai arzikin ta kai $150 biliyan kuma ya tara ta ne ta hanyar kasuwancin kayan alfarma. Mazaunin Paris ne.

4. Bill Gates: tarin dukiyarsa ta kai $124 biliyan kuma ya tara ta ne ta hanyar Microsoft. Mazaunin Medina ne dake Washington.

5. Mark Zuckerberg: Yana da dukiyar da ta kai $97 biliyan kuma ya sameta ta hanyar Facebook. Mazaunin Palo Alto ne dake California.

6. Warren Buffett: Dukiyarsa ta ka $96 biliyan kuma Berkshire Hathaway ne tushen dukiyar. Mazaunin Omaha ne a Nebraska.

7. Larry Ellison: Tarin dukiyarsa ta kai $93 biliyan kuma ya tara ne ta hanyar kasuwancin na'ura mai kwakwalwa. Mazaunin Lanai ne dake Hawaii.

8. Larry Page: Ya tara dukiyar da ta kai $91.5 biliyan kuma ya sameta ta ta Google. Mazaunin Pali Alto ne dake California.

9. Sergey Brin: Dukiyarsa ta kai $89 biliyan kuma ya sameta ne ta ne Google. Mazaunin Los Altos ne dake California.

10. Mukesh Ambani: Dukiyarsa ta kai $84.5 Biliyan. Ya tara dukiyarsa ta hanyoyi masu yawa kuma mazaunin garin Mumbai ne dake kasar India.

A wani labari na daban, an samu labarin yadda wasu 'yan bindiga suka budewa wani shugaba na jam'iyyar APC wuta, Olorogun Ovoke Shasha a garin Ughelli dake jihar Delta.

Vanguard ta bayyana yadda dan siyasar yake tsaka da tukin motarsa kirar Highlander SUV kwatsam dai yaji ruwan alburusai a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu.

Majiyoyi sun tabbatar da yadda harbin ya ji masa raunuka a kirjinsa kuma aka yi gaggawar zarcewa dashi asibiti domin kulawa da lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel