Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

- Wani dan Najeriya ya wallafa hotunan wata shukar mangwaro a gidansu na kauye kuma hakan ya burge kowa

- A cewarsa, duk da bishiyar tana samar da dubannin mangwarori amma da dama asararsu ake yi

- Jama'a da dama sun shawarce shi da yayi wani abu akan wannan asara da suke tafkawa ta hanyar amfana dasu

Wani mutum dan Najeriya mai amfani da suna celestocalculus ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a kan wata bishiyar mangwaron gidansu na kauyensu.

A cewarsa, bishiyar tana samar da dubannin magwarori a kowacce shekara.

A wallafar da yayi a ranar Lahadi, 4 ga watan Afirilu ya wallafa hotunan bishiyar magwarori 92 daya katso . A cewarsa dayan bangaren bishiyar yana da mangwarori kurin 1000, yana nuna takaicin yadda suke zama asara sakamakon yadda jama'a basa shan mangwaron.

Wasu mutane sun bukaci ya aika musu da mangwarorin.

KU KARANTA: Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa

Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000
Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000. Hoto daga @celestocalculus
Asali: Twitter

Mutumin ya yi wa iyaye da kakanninsa da suka shuka bishiyar addu'o'i sakamakon dasa bishiyar mai albarka. Har cikin barkwanci yake cewa yadda bishiyar take samar da mangwarori, ya kusa zama biloniya da kudin mangwaro idan aka gane kauyensu.

Nan da nan jama'a suka fara tsokaci iri-iri, wani amakac cewa yayi: "Ka taimaka ya kawo min mangwaro Mai yawa."

Officialdayan cewa tayi: "Kana zuwa Onitsha kuwa ko kuma yaushe zaka zo Enugu? Duk naji ina son sha kamar mai ciki."

Cewar ebuukanary1: "Kai! mangwarorin jamus masu burgewa."

T0bey kuwa cewa yayi: "Muna kiransu da mangwarorin jamus, ba a samunsu a inda nake."

KU KARANTA: Da duminsa: Ku mitsike min dukkan mambobin IPOB, Sifeta Janar Adamu

A wani labari na daban, ranakun zagayowar haihuwa su kan zo da albarkatu iri-iri musamman yadda mutane suke nuna wa mai shagali ko bikin so da kauna ta hanyar bayar da kyautuka na ban mamaki.

Wata 'yar Najeriya mai suna Miss P, wacce ranar haihuwarta ta zagayo taga ruwan naira, inda saurayinta ya gwangwajeta da kyauta mai yawa. Kamar yadda ta wallafa, ta roki saurayinta kudi amma bata yi tunanin zai bata masu yawa haka ba.

Ta wallafa wani bidiyo wanda aka ga tana shagalin a gida yayin da sauti mai dadin saurara ya bude ko ina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel