Shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano ya nada hadimai 55

Shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano ya nada hadimai 55

- Shugaban karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano ya dauki masu bashi shawarwari na musamman da hadimai 55 aiki

- Yayin da Hassan Garban Kauye Farawa yake rantsar dasu, ya ce ya daukesu aiki ne don tabbatar da shirin Ganduje na fatattakar talauci a jihar

- Ya shawarci sababbin ma'aikatan dasu zage damtse kuma suyi aiki tukuru don tabbatar da sun bunkasa karamar hukumar Kumbotso

Shugaban karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Hassan Garban Kauye Farawa, ya dauki hadimai 55.

Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin da yake rantsar dasu, Farawa ya ce ya yi hakan ne don tabbatar da manufar Gwamna Abdullahi Ganduje na fatattakar fatara a jihar.

Ya horesu da su zage damtsensu wurin aiwatar da duk wasu ayyuka da zasu kawo cigaba ga karamar hukumar.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

Shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano ya nada hadimai 55
Shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano ya nada hadimai 55. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Daukar hadimai 55 yana daya daga cikin hanyar fatattakar talauci daga jihar Kano na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje musamman ga matasa a wannan halin tsanani da wahala da ake ciki," a cewarsa.

Shugaban karamar hukumar yayi kira garesu da su yi iyakar kokarinsu na ganin sun kare mutuncin karamar hukumar Kumbotso da jihar Kano.

Kansilan gundumar Gurungawa dake karamar hukumar Kumbotso ya dauki hadimai 18, al'amarin da ya janyo cece-kuce.

Daily Trust ta ruwaito yadda kansilan ya sadaukar da albashinsa na farko don taimaka wa mutane 100 masu fama da nakasa a gundumarsa.

KU KARANTA: Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes

A wani labari na daban, Ranakun zagayowar haihuwa su kan zo da albarkatu iri-iri musamman yadda mutane suke nuna wa mai shagali ko bikin so da kauna ta hanyar bayar da kyautuka na ban mamaki.

Wata 'yar Najeriya mai suna Miss P, wacce ranar haihuwarta ta zagayo taga ruwan naira, inda saurayinta ya gwangwajeta da kyauta mai yawa.

Kamar yadda ta wallafa, ta roki saurayinta kudi amma bata yi tunanin zai bata masu yawa haka ba. Ta wallafa wani bidiyo wanda aka ga tana shagalin a gida yayin da sauti mai dadin saurara ya bude ko ina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel