Wani tsohon Sanatan jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya jiya Talata
- Tsohon sanata daga jihar Filato ya rasu sakamakon wata jinya da ya shafe shekara guda
- Danginsa sun bayyana cewa, ya yi fama da rashin lafiyar da ta sa ya bar Najeriya neman magani
- Mamacin dai shine sanatan da ya taba wakiltar Filato ta tsakiya a majalisar dattijai a 2007
Tsohon Sanata Sati Gogwim na Filato ya rasu a ranar Talata bayan fama da rashin lafiya, wata majiya daga dangi ta ce, jaridar Punch ta ruwaito.
Mista Williams Gogwim, kani ga marigayin ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Pankshin a ranar Laraba.
“Yayana ba shi da lafiya tun shekarar da ta gabata kuma a watan Disamba ya bar kasar don neman magani a kasashen waje, dawowarsa kenan ranar Lahadi, 4 ga Afrilu.
“Ya dawo da dan karfi kadan, har zuwa safiyar yau kafin lokacin da rashin lafiyan ya karu, wanda hakan ya tilasta mana garzayawa da shi zuwa Rayfield Medical Center.
"Abin takaici da zuwa asibitin aka tabbatar da mutuwarsa," in ji shi.
KU KARANTA: Tsawon mako guda kenan Korona ba ta yi kisa ba a Najeriya
Williams ya ce dangin sun dauki mika dangana da mutuwarsa, ya kara da cewa a matsayinsu na Kiristoci na gaskiya, sun yi imani cewa Allah ne ya kira shi zuwa gidan gaskiya.
"Za mu yi kewar kaunarsa da kulawarsa a matsayin dan uwa, uba, kawu kuma mai tallafawa," in ji shi.
Williams ya ce dangin sun yi mamakin rasuwarsa kuma za su tattauna game da jana'izarsa nan ba da jimawa ba.
An zabi Gogwim a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Tsakiya a 2007 kuma ya kwashe shekaru hudu a Majalisar Kasa kafin ya sha kaye a hannun Sanata Joshua Dariye a 2011.
Gogwim ya fito ne daga Kauyen Dawaki da ke Karamar Hukumar Kanke a Filato.
Ya yi ritaya a matsayin Manjo a Sojan Najeriya kafin ya shiga siyasa kuma ya zama Sanata a 2007.
KU KARANTA: Yawaitar hatsarin mota yasa Dangote ya kaddamar da cibiyar horar da direobi
A wani labarin, Alkalumman da hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ke fitarwa game da cutar korona a kasar ya nuna cewa tsawon mako daya kenan cutar ba ta yi kisa ba a fadin kasar, BBC ta rahoto.
Alkalumman wadanda cutar ta kashe ba su sauya ba tun daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu inda cutar ta kashe jimillar mutum 2,058 tun shigowarta.
Alkalumman da hukumar ta fitar ranar Talata sun nuna cewa karin mutum 58 da sun kamu da cutar korona a Najeriya.
Asali: Legit.ng