Azumin Ramadana: Saudiyya ta hana sahur da buda-baki a masallatan ƙasar

Azumin Ramadana: Saudiyya ta hana sahur da buda-baki a masallatan ƙasar

- Kasar Saudiyya ta sanar da hana yin bude-baki da sahur a masallatan kasar a lokacin Azumin watan Ramadana na bana

- Hakazalika ta dakatar da yin I’tikaf daga cikin matakan dakile yaduwar annobar korona

- Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci ta kasar ta kuma bayyana cewa za a shigar da masallatan da ake yin sallar Juma'a cikin jerin wadanda za su yi sallar Idi

Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci ta kasar Saudiyya ta sanar da hana yin bude-baki da sahur a masallatan kasar a lokacin Azumin watan Ramadana na bana.

Kamar yadda aka saba duk shekara a kasa mai tsarki, a kan yi taron bude baki da sahur a masallatai da ke birnin.

KU KARANTA KUMA: Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda zai ziyarci Imo

Azumin Ramadana: Saudiyya ta hana sahur da buda-baki a masallatan ƙasar
Azumin Ramadana: Saudiyya ta hana sahur da buda-baki a masallatan ƙasar Hoto: @Zeeeqasim
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwar da shafin @hsharifain ya wallafa a Twitter a ranar Talata, 6 ga watan Maris, ta kara da cewa an dauki matakin ne saboda annobar cutar korona da duniya ke fama da ita.

Sanarwar ta ce nan gaba kadan za a sanar da yadda tsarin sallolin Taraweeh da Tahajjud za su kasance a lokacin azumin.

Har wa yau, za a shigar da masallatan da ake yin sallar Juma'a cikin jerin wadanda za su yi sallar Idi, saboda rage cunkoson mutane.

Ga yadda ta wallafa a shafin nata:

"Da dumi-dumi!! Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci ta yanke hukunci game da # Ramadan ga Masallatai a duk fadin Saudiyya:

"1. Za a ci gaba da dakatar da bude-baki, sahur da I’tikaf a wannan shekarar

"2. Za a sanar da Shawara a kan Taraweeh / Tahajjud

"3. Za a shigar da masallatan da ake yin sallar Juma'a cikin jerin wadanda za su yi sallar Idi."

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Babban hafsan sojin sama ya bayyana lokacin da ta'addanci zai zo karshe a Najeriya

A baya mun ji cewa masu zuwa aikin Umrah a wannan shekarar da ake ciki za su gamu da wasu bakin dokoki da maniyyatan kasa mai tsarkin ba su san da su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an kafa wasu sababbin sharuda da dokoki da masu aikin Umrah za su bi wajen ibadar su a wannan shekarar ta bana.

Bayanan da aka fitar a shafin ‘Inside the Haramain’ mai yada labaran abin da su ka shafi aikin Hajji da Umrah ne su ka fito da wadannan dokoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng