Mutum 8 sun hallaka, da dama sun jikkata a wani sabon harin yan bindiga a jihar Kaduna

Mutum 8 sun hallaka, da dama sun jikkata a wani sabon harin yan bindiga a jihar Kaduna

- Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa an kashe mutane 8, kuma an jikkata mutum huɗu a wasu hare-hare da suka kai a Kajuru da Kachia

- Kwamishinan yaɗa labarai da kuma harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin

- Hukumomin tsaro na gudanar da bincike akan lamarin, kuma su kamo waɗanda suka kawo harin

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin yan fashi ne sun kashe mutane takwas sun jikkata wasu huɗu a wasu hare-hare da suka kai a yankin ƙaramar hukumar Ƙajuru da Kachia.

KARANTA ANAN: CAN ta caccaki Buhari: Ba a zabe ka don kazo ka yi korafi kan shugabancin baya ba

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Mr. Samuel Aruwan, ya tabbatar da kisan mutanen a wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Kaduna.

Aruwan ya ce ɗaya daga cikin harin shine wanda yan bindigar suka tare hanyar Kaduna zuwa Kachia, a dai-dai ƙauyen Kaɗanye dake ƙaramar hukumar Kajuru.

Yan bindigar sun buɗe wuta ga wata motar bas ɗauke da fasinja, da kuma wata babbar motar dauko kaya mai ɗauke da katako.

Kwamishinan ya ce an kashe mutum biyar a wannan harin sannan kuma aka jikkata mutum uku, waɗanda a yanzun haka suna asibiti suna karɓar magani.

Yan fashi sun Hallaka mutum 8, sun kuma jikkata mutane da dama a jihar Kaduna
Yan fashi sun Hallaka mutum 8, sun kuma jikkata mutane da dama a jihar Kaduna Hoto: @Samuelaruwan
Source: Twitter

Aruwan ya ƙara da cewa a ɗayan harin kuma, yan bindigar sun tare hanyar Kaduna zuwa Kachia a dai-dai mahaɗar hanya dake Doka, suka buɗewa wata babbar mota wuta, suka kashe direban motar.

KARANTA ANAN: Saurayi ya gwangwaje budurwar da N24m ranar zagayowar haihuwarta, 'yan mata sun gigice

Kwamishinan ya cigaba da cewa yan bindigar basu tsaya nan ba, sun shiga wata rugar fulani, haka kuma suka kashe mutum ɗaya kafin daga bisani su tasa shanu 180.

Samuel Aruwa ya ce gwamnan jihar baiji dadin abinda ke faruwa ba kuma ya yi jaje ga iyalan waɗanda abun ya shafa.

Gwamnan ya kuma yi addu'a Allah ya jikansa ya kai haske ƙabarinsa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa hukumomin tsaron jihar na nan na cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

A wani labarin kuma Ganduje ya zabtare rabin albashinsa da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya rage wa dukkan masu rike da mukaman siyasa albashi a watan Maris.

Gwamnatin jihar Kano ta ce an dauki wannan matakin ne saboda kudaden da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a duk wata ya ragu.

Source: Legit.ng

Online view pixel