Rikicin addini a Gombe: Gwamna Yahaya ya tallafawa wadanda rikici ya rutsa dasu
- Gwamnatin jihar Gombe ta ba wadanda rikin Billiri ya shafa tallafin kayayyakin abinci
- Gwamnatin ta ce tana ci gaba da tantace wadanda rikicin ya rutsa dasu don biyan diyya
- Hakazalika ta bayyana wannan mataki na tallafi da rage radadi ga wadanda abin ya shafa
Gwamnatin jihar Gombe ta raba kayayyakin tallafi ga mutanen da rikicin kwanan nan ya shafa a karamar hukumar Billiri na jihar, Leadership ta ruwaito.
An gudanar da aikin raba kayan tallafin ne ta hannun wani kwamiti na musamman da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya kafa tare da tabbatar da an samu raba-daidai da adalci a raba tallafin.
Da yake zantawa da manema labarai yayin rabon kayan a garin Billiri, Shugaban kwamitin, Hon. Ibrahim Dasuki Jalo ya ce kimanin mutane 2,000 da aka zakulo ne aka yi niyyar tallafawa.
Ya ce kafa kwamitin rabon kayayyakin agajin da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ya biyo bayan barnata dukiyar wasu mazauna da ba su ji ba su gani ba a garin Billiri yayin rikicin kwanan nan kan nadin sabon Mai Tangle.
KU KARANTA: CAN ta caccaki Buhari: Ba a zabe ka don kazo ka yi korafi kan shugabancin baya ba
Ya ce, "Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya cikin hikimarsa ya ga bukatar kawo tallafi ga wadanda rikicin na kwanan nan ya rutsa da su a garin na Billiri ta hanyar samar da wadannan kayayyakin tallafi."
Ya kuma bayyana cewa, tallafin somin-tabi ne kafin kwamitin da aka nada don tantance barnar ta ba da rahoton bayar da diyya ga wadanda lamarin ya shafa.
Hon Dasuki Jalo ya bayyana karara cewa sharuddan aikin kwamitin nasa sun takaita ne ga rabon kayan agaji domin rage radadi ga wadanda abin ya shafa yayin da za a kayyade diyyar mutanen da abin ya shafa.
“Kamar yadda kuke ganin kayayyakin tallafi da ake raba wa mutanen da abin ya shafa sun hada da buhunan shinkafa, sukari, garri, katan din taliyar indomie da sauran nau’ikan taliya," in ji shi.
Da yake nuna gamsuwa kan yadda aka gudanar da aikin, Hon Dasuki Jalo ya yi amannar cewa kayayyakin abincin za su taimaka wajen saukake wahalhalu ga wadanda abin ya shafa da kuma karfafa su a rayuwarsu.
Ya yaba da jajircewar masu ruwa da tsaki da ke cikin aikin rarraba kayan tallafin daga ko'ina a fadin jihar.
Wasu da suka ci gajiyar tallafin wadanda suka yi magana da manema labarai yayin rabon, sun nuna farin cikinsu da godiyar su ga gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya game da aikin.
Taron wanda aka gudanar a filin wasa na garin Billiri an gudanar da shi ne karkashin kulawar mambobin kwamitin, jami’an karamar hukumar ta Billiri da kuma jami’an tsaro.
KU KARANTA: An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai
A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce kawo yanzu an tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 170 daga ‘yan Najeriya mutanen kirki, a matsayin gudummawa ga wadanda iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.
Masari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar dattawan Katsina karkashin jagorancin shugabanta, Ahmad Muhammad-Daku a gidan gwamnatin Katsina, ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.
"Kodayake har yanzu ba mu bude kofofin don ba da gudummawa ga wadanda bala'in gobarar ya shafa ba, mun kaddamar da kwamiti don gano musabbabin tashin gobarar", in ji shi.
Asali: Legit.ng