Yajin aiki: Minista Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa

Yajin aiki: Minista Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa

- Ministan ilimi a Najeriya ya nemi kungiyar malaman jami'o'i zaman gaggawa gobe Talata

- Manufar zaman shine shawo kan yajin aikin da kungiyar kwadago ke shirin yi kwanan nan

- Kungiyar a baya dai ta janye wani dogon yajin aiki da ta share watanni tana yi a kasar

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gayyaci shugabannin kungiyar malaman jami'o'in (ASUU), zuwa wani taron gaggawa, Vanguard News ta ruwaito.

Taron wanda aka shirya gobe Talata, yana zuwa ne bayan barazanar da kungiyar kwadago ta yi na shiga wani yajin aikin.

Bayanin hakan ya faru ne a yammacin Litinin yayin da daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar, Bem Goong, ya ruwaito Ministan yana bayanin cewa taron "an shirya shi ne domin yajin aikin dake tafe."

KU KARANTA: An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai

Yajin aiki: Minsta Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa
Yajin aiki: Minsta Adamu ya gayyaci ASUU zuwa taron gaggawa Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sanarwar ta ce: “Ministan Ilimi Adamu Adamu ya gayyaci kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) taron gaggawa bayan barazanar shiga wani yajin aikin.

“Taron gaggawa zai gudana ne a gobe, 6 ga watan Afrilu 2021 da karfe 11:00 na safe a Hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.

“Da yake bayanin dalilin taron na gaggawa, Ministan ya ce taron na da niyyar kare tsundumawa yajin aikin ne da ke tafe.

“Za a tuna cewa ASUU ta fitar da sanarwar yajin aiki a kan abin da kungiyar kwadagon ta bayyana a matsayin kin Gwamnati a aiwatar da wasu yarjejeniyoyi da aka kulla tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayya.

"ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi a watan Janairun bana.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta gayyaci mambobin kungiyar likitocin kasa (NARD) zuwa wani ganawa da nufin kaucewa yajin aikin da suka shirya farawa a ranar Alhamis, 1 ga Afrilu, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin ma’aikatar, Charles Akpan, ya ce za a gudanar da zaman ne da karfe 3 na yammacin Laraba, a hedkwatar ma’aikatar dake Abuja.

Yayin da Ngige ne zai jagoranci wakilan gwamnati, mambobin kungiyar ta NARD ana sa ran shugabanta ne, Uyilawa Okhuaihesuyi zai jagorance ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel