Wasu 'Yan Bindiga sun sace yan China guda biyu, sun kuma harbe jami'an tsaro a Jihar Osun

Wasu 'Yan Bindiga sun sace yan China guda biyu, sun kuma harbe jami'an tsaro a Jihar Osun

- Rundunar Yan sanda a jihar Osun ta tabbatar da sace wasu yan ƙasar China mazauna Najeriya guda biyu a ranar litinin 5 ga watan Afrilu

- Yan sandan sun ce an sace mutanen biyu ne a wurin haƙar ma'adanan ƙasa dake ƙauyen Okepa/Itikan dake jihar ta Osun

- Kwamishinan yan sandan jihar ya haɗa jami'an tsaron haɗin guiwa don ganin an ceto mutanen an kuma kamo yan bindigar

Rundunar yan sanda reshen jihar Osun sun tabbatar da sace wasu yan ƙasar China mazauna Najeriya a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2021

Hukumar ta bayyana cewa yan bindigar sun sace Zhao Juan, dan shekara 33 da kuma One Wen, ɗan kimanin shekara 50 a wajen haƙar ma'adanai na jihar.

An sace mutanen biyu a wajen haƙar ma'adanai dake ƙauyen Okepa/Itikan ƙaramar hukumar Atakumosa ta yamma a jihar Osun a ranar Litinin 5 ga watan Afrilu.

Wasu 'Yan Bindiga sun sace yan China dake zaune a Najeriya, sun harbe jami'an tsaro a Jihar Osun
Wasu 'Yan Bindiga sun sace yan China dake zaune a Najeriya, sun harbe jami'an tsaro a Jihar Osun Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai hari wurin ne da yawan su, suka fara musayar wuta da jami'an tsaron wurin na tsawon awa ɗaya kafin daga bisani su ci ƙarfin jami'an tsaron.

KARANTA ANAN: Harin yan daba: An tsaurara matakan tsaro yayinda Sufeto Janar na yan sanda zai ziyarci Imo

A jawabin da mai magana da yawun yan sandan jihar, Yemisi Opalola ya yi, ya ce yan bindigar sun harbe jami'an tsaro masu zaman kansu guda biyu kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen.

Daga faruwar lamarin ne, kwamishinan yan sandan jihar, CP Olawale Olokode, ya tura jami'an tsaro cikin gaggawa zuwa wurin da abun ya faru.

Kwamishinan ya tura jami'an tsaro da suka haɗa da, yan sanda, jami'an sa kai na JTF, da sauran jami'an tsaro waɗanda suka shiga neman yan bindigar don kuɓutar da waɗanda aka sace da kuma kama waɗanda suka yi wannan aika-aika.

A wani labarin kuma Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya karɓi tawagar masu sauya sheka daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa jam'iyya mai mulkin jihar APC

Gwamnan wanda tsohon gwamnan jihar, Segun Adesegun, ya wakilta ya bayyana jin daɗinsa da wannan cigaba da jam'iyyarsa ta APC ke samu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel