Yanzu-Yanzu: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2021

Yanzu-Yanzu: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2021

- Hukumar shirya jarrabawa ta WAEC ta saki sakamakon WASSCE Private na shekarar 2021

- Shugaban WAEC na Nigeria, Mr Patrick Areghan, ne ya bada sanarwar a yau Talata 6 ga watan Afrilu

- Cikin dalibai 7,289 da suka rubuta jarrabawar, dalibai 2,195 ne suka samu credit a darrusa 5 da suka hada da lissafi da Ingilishi

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta, WAEC, ta fitar da sakamakon jarrabawar Private ta 2021 na farko, The Punch ta ruwaito.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata, Shugaban WAEC na Nigeria, Mr Patrick Areghan, ya ce an tsara jarrabawar ne domin taimakawa wadanda ke neman shiga makarantun gaba da sakandare samun sakamakonsu a kan lokaci.

DUBA WANNAN: Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

Yanzu-Yanzu: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2021
Yanzu-Yanzu: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2021. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya ce, "Wannan jarrabawar ita ma na kasa da kasa ne. Wannan shine karo na 4 a Nigeria, an fara ne a shekarar 2018. An bullo da jarrabawar ne domin taimakawa masu neman shiga makarantun gaba da sakandare samun sakamako kan lokaci.

"Kididdigar alkalluman ya nuna cewa dalibai Dubu bakwai da dari biyu da tamanin da tara (7,289) suka rubuta jarrabawar.

"Dubu biyu da dari tara da talatin da takwas (2,938) wato kashi 40.31 cikin 100 sun samu kredit da abinda ya fi hakan a darrusa biyar (da turanci da lissafi ko akasin haka; daga cikinsu Dubu daya da dari uku da casa'in da shida (1,396) maza ne wato (47.52%) sannan Dubu daya da dari biyar da arba'in da biyu mata ne (52.48%).

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

"Dubu biyu da dari da casa'in da biyar (2,195) wato kashi 30.11 sun samu kredit a akalla darrusa 5 ciki har da lissafi da Ingilishi.

"Daga cikin wannan adadin, 1,074 maza ne yayin da 1,121 mata ne. Adadin daliban da suka rubuta WASSCE Private a 2019 da 2020 da suka samu kredit a darrusa 5 ciki har da lissafi da Ingilishi, 26.08% da 32.23% kamar yadda aka jero su. Hakan na nufin a bana an samu ragin 2.12%."

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel