Sauyin Sheƙa: Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar

Sauyin Sheƙa: Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar

- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya karɓi tawagar masu sauya sheka daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa jam'iyya mai mulkin jihar APC

- Gwamnan wanda tsohon gwamnan jihar, Segun Adesegun, ya wakilta ya bayyana jin daɗinsa da wannan cigaba da jam'iyyarsa ta APC ke samu

- Ya ce wannan yawaitar sauya shekar babbar alama ce da ke nuni da cewa jama'ar jihar sun gamsu da salon mulkin jam'iyyar ta APC shiyasa suke ƙara amincewa da ita.

Jam'iyya mai mulki a jihar Ogun ta karɓi tawagar yan jam'iyyar hamayya ta PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a garin Ijebu Igbo.

KARANTA ANAN: Labari da ɗumi-ɗuminsa: ASUP ta fara yajin aikin sai baba ta gani a Nigeria

Tsohon mataimakin gawmnan jihar, Segun Adesegun, ya karɓi waɗanda suka sauya shekar, a tare dashi akwai mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar ta fannin al'amuran siyasa,Tunji Egbetokun.

An karɓi waɗanda suka sauya shekar ne a wajen taron ƙungiyar mazaɓun jihar na jam'iƴyar APC a Ijebu Igbo, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Sauyin Sheƙa: Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar
Sauyin Sheƙa: Gwamnan Jihar Ogun ya karbi tawagar yan Jam'iyyar PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar Hoto: @dabiodunMFR
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Wani Inyamuri ne ya damfare ni kudi N450 miliyan shiyasa nayi barazanar kashe kaina - Ummi Zeezee

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, wanda tsohon mataimakin gwamnan, Segun Adesegun, ya wakilta ya ce wannan yawaitar sauya sheƙar da ake samu yana nuna cewa jama'ar jihar sun gamsu da salon mulkin gwamnatin jihar.

"Wannan alama ce ta kyakkyawan mulkin mu. Masu sauya shekar sun wuce tunanin mu wajen ƙoƙarin yin rijista ta jam'iyyar mu." inji gwamnan.

Ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar APC na da adalci, kuma zata cigaba da tafiya da kowa a gwamnatin ta.

A wani labarin kuma Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yana da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa

'Yan sanda a jihar Adamawa sun yi ram da wani matashi ɗan shekara 30 da zargin kashe wani dattijo ɗan shekara 57 a ƙauyen Bandasarga ƙaramar hukumar Ganye.

Matashin dai ya dawo gidansa ne ya sami mutumin ɗan shekara 57 a gidansa da daddare, daga nan ya fara zarginsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel