Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yana da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa

Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yana da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa

- 'Yan sanda a jihar Adamawa sun yi ram da wani matashi ɗan shekara 30 da zargin kashe wani dattijo ɗan shekara 57 a ƙauyen Bandasarga ƙaramar hukumar Ganye

- Matashin dai ya dawo gidansa ne ya sami mutumin ɗan shekara 57 a gidansa da daddare, daga nan ya fara zarginsa

- Kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya ce mutanen yankin da abun ya faru su kwantar da hankalinsu.

Rundunar yan sandan ƙasar nan reshen jihar Adamawa ta kama wani ɗan shekara 30 da zargin kashe wani dattijo ɗan shekara 57 a duniya.

KARANTA ANAN: Fusatattun matasa sun zane matasan da suka yi zanga- zangar kin Buhari a Kogi

Matashin ya kashe dattijon ne saboda yana zargin cewa yana da wata boyayyar alaƙa da matarsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wanda aka kama ɗin mai suna, John Samuel, mazaunin ƙauyen Bandasarga ƙaramar hukumar Ganye, a jawabin yan sanda, ya dawo gida da misalin ƙarfe 11:00 na dare sai ya haɗu da dattijon a cikin gidansa.

Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yan da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa
Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yan da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa Hoto: @PoliceNG_News
Asali: Twitter

Daga nan kuma sai Samuel ya fara zargin mutumin da cewa yana zuwa ne suna ƙulla boyayyar alaƙa da matarsa.

Bayan haka sai Samuel yaje ya caka mishi wuƙa, ya tafi ya barshi cikin jini, kamar yadda mai magana da yawun yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya faɗa.

KARANTA ANAN: JIBWIS ta yi kira ga Gwamnatin shugaba Buhari da ta ƙara ƙaimi a yakin da take da yan ta'adda

Nguroje, ya ƙara da cewa an yi gaggawar kai mutumin mai suna Yaji Lawal zuwa asibiti amma daga baya aka tabbatar da ya mutu.

Ya ce daga nan sai jami'an yan sanda suka koma suka kama wanda ya yi wannan aika-aika, wanda mahaifi ne ga 'ya'ya uku.

Kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin tsananta bincike kan lamarin, kuma ya yi kira ga al'ummar yankin da abun ya faru da su kwantar da hakulansu.

A wani labarin kuma Gwamna El-Rufai zai hukunta duk wanda ya yi sulhu da ‘Yan bindiga a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu ya na magana da wadanda su ka sace yaran makaranta 39 da aka sace.

Kwanakin baya wasu miyagun ‘yan bindiga su ka shiga babbar makarantar gandun dabbobi da ke garin Afaka, jihar Kaduna, su ka sace dalibai kusan 40.

Asali: Legit.ng

Online view pixel