Labari da ɗumi-ɗuminsa: ASUP ta fara yajin aikin sai baba ta gani a Nigeria
- Kwallejojin Fasaha (Polytechnic) na Nigeria sun fara yajin aikin sai baba ta gani a yua Talata 6 ga wantn Afrilun 2021
- Anderson Ezeibe, Shugaban kungiyar Malaman Kwallejojin Fasaha ne ya sanar da hakan a Abuja
- Ezeibe ya ce makarantun za su kasance a rufe har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu
Shugabannin kungiyar malaman kwalejin fasaha na ƙasa, ASUP, ta sanar da fara yajin aikin yi na sai baba ta gani a kasa baki ɗaya.
Anderson Ezeibe, shugaban kungiyar ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a ranar Talata a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna
Ya ce mambobin kungiyar sun amince rufe dukkan Kwalejin fasaha da ke kasar har sai an biya musu buƙatunsu.
Hakan ne zuwa ne duk da yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na ganin Kwalejojin ba su tafi yajin aikin ba.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara
Tunda farko Ministan Ilimi Adamu Adamu, a ranar Litinin ya gayyaci ASUP ganawar gaggawa bayan barazanar da ta yi na fara sabon yajin aiki.
A cewar kakakin ma'aikatar ilimi, Ben Bem Goong, an shirya yin taron ne a ranar Talata misalin karfe 10 na safe a hedkwatar ma'aikatar a Abuja.
Amma Ezeibe, yayin taron manema labarai ya ce mambobin kungiyar sun amince a rufe dukkan kwallejojin ilimi a kasar daga karfe 12.00 na daren ranar 6 ga watan Afrilu.
ASUP ta ce ta tafi yajin aikin ne saboda rashin aiwatar da abubuwan da ke cikin rahoton NEEDS na shekarar 2014 da kuma rashin biyan wasu kudade na inganta sassa da dama a makarantun duk da tabbacin da aka basu a 2017.
Kungiyar ta kuma ce rashin kafa kwamitin gudanarwa a kwallejojin fasaha na tarayya da jihohi ya janyo tsaiko wurin gudanar da ayyuka a makarantun tun Mayun 2020.
Ezeiba ya kara da cewa, "rashin biyan allawus na watanni 10 daga albashi mafi karanci da ma'aikatan kwallejojin fasahar ta tarayya da jihohi" na daga cikin dalilan fara yajin aikin duk da cewa an bada umurnin a biya kudaden tun Disambar 2019.
Ya kuma ambaci cin mutuncin mambobin kungiyar a wasu makarantu kamar Institute of Management and Technology, Enugu; Federal Polytechnic, Mubi; da Rufus Giwa Polytechnic, Owo.
A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.
Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.
Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.
Asali: Legit.ng