Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno

Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno

- A tsakar daren Lahadi 'yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa sansanin sojoji farmaki

- Majiyoyi da dama sun tabbatar da yadda 'yan Boko Haram suka yi musayar wuta da sojojin

- Al'amarin ya faru ne a karamar hukumar Gwoza, jihar Borno inda sojojin suka kashe 'yan Boko Haram 12

Rundunar sojin Najeriya ta bataliya ta 192 dake karamar hukumar Gwoza a jihar Borno sun samu nasarar kashe a kalla wasu 'yan ta'adda 12 da ake zargin 'yan Boko Haram ne, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da tsakar daren Lahadi ne 'yan ta'addan suka kaiwa sansanin sojojin farmaki. Majiyoyi da dama sun sanar da The Cable cewa sojojin sun yi musayar wuta dasu.

"Rundunar Tango 9 sun yi gaggawar mayar da harin da 'yan ta'adda suka kai musu har suka kashe mutane 7 take yanke, hakan yasa suka ja da baya," Kamar yadda majiyar ta tabbatar.

KU KARANTA: Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige

Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno
Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaban kasan Japan ya nada 'ministan kadaici' bayan hauhawar kashe kai

"Sannan bayan zagaye gaba daya kewayen gurin tare da dasa bama-bamai wuri-wuri, sun kara samun nasarar kashe wasu 5 din.

"Rundunar ta samu nasarar kwatar bindigogi kirar AK 47 guda 10, bindigar harbo jirgin sama da kuma sani babur tare da sauran makamai."

Ba a samu zantawa da kakakin rundunar sojin Najeriya ba, Mohammed Yerima, balle a ji ta bakinsa.

A watannin da suka gabata, sojoji suna ta samun nasarori iri-iri musamman a arewa maso gabas wurin yakar 'yan Boko Haram.

A wani labari na daban, alamu sun nuna cewa jirgin yakin sojojin Najeriya da ya bace an gan shi a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno mai nisan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Duk da hukumar rundunar sojin kasan bata riga ta tabbatar da wannan cigaban ba, majiyoyi a ranar Juma'a sun ce an ga jirgin yakin na shawagi a kauyukan Goni Kurmiri da Njimia bayan ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa da yayi.

Majiyoyin sun ce, har yanzu ba a samu labarin inda matukin jirgin da abokin aikinsa suke ba, Channels TV ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel