Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari

Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari

- Jaruman sojoji da 'yan sanda sun nuna jajircewa yayin da 'yan ta'adda suka kai wani hari Borno

- A ranar Juma'a, 2 ga watan Afirilu ne 'yan Boko Haram suka kaiwa tawagar gwamnan jihar farmaki

- Jami'an tsaron sun nuna jarumtarsa ta hanyar kashe 'yan ta'addar guda 7 bayan sunyi musayar wuta

Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno farmaki a ranar Juma'a, 2 ga watan Afirilu kan titin Monguno zuwa Nganzai.

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, jami'an tsaro sun samu nasarar mayar da harin. Sojoji da 'yan sanda sun hada karfi da karfe wurin ragargazar 'yan ta'addan.

Tawagar tana tsaka da dawowa daga Monguno sai ga 'yan ta'adda da bindigogi sun fara yi musu ruwan wuta. A nan sojoji da 'yan sanda suka fara ragargazarsu, sai da suka samu nasarar kashe 'yan ta'adda 7 take yanke duk da miyagun makaman da suke rike dasu.

KU KARANTA: Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari
Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari. Hoto daga @GovBorno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa

'Yan sandan da CSP Muhammed Ibrahim ya jagoranta da tawagar sojojin sun samu damar damkar daya daga cikin 'yan ta'addan baya ga wadanda suka kashe.

Sakamakon fadan, sai da sojoji 3 suka samu raunuka sannan aka yi gaggawar tafiya dasu asibiti.

Cikin manyan mutanen da suke tawagar akwai Antoni janar na jihar Borno, Kakashehu Lawal; kwamishinan jihar, Mustapha Gubio da kwamishinan kananan hukumomi da lamurran masarautu, Alhaji Mai-Mele.

A wani labari na daban, sojojin saman Najeriya sun musanta iƙirarin da ƴan ƙungiyar boko haram suka yi a wani bidiyo na harbo jirgin yaƙin sojojin da aka nema aka rasa tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Boko haram sun saki wani bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka harbo jirgin yaƙin.

Sa idai babban jami'in hulɗa da jama'a na sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya musanta maganar wannan bidiyon da ƴan Boko Haram suka saki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel