Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

- Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana wa duniya cewa shekaru ba komai bane

- Obasanjo yana bayyana hakan ne ta hanyar kwasar rawa da salon motsa jiki masu ban sha'awa

- Yana yawan bayyana tsuke da ƙananun kaya da tabarau irin na zamani wanda hakan yake ɓoye tsufarsa

Alamu sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya gwada wa ƴan Najeriya cewa shekaru ba a bakin komai suke ba.

Kamar yadda alamu suka nuna, tsohon wanda ya wuce shekaru 70 a duniya yana kwasar rawa cikin nishaɗi da ƙarfin jiki, Daily Trust ta ruwaito.

Jama'a sun yi ta cece-kuce bayan ganin shi tsuke da wasu ƙananun sutturu da baƙar hula mai ban sha'awa tare da tabarau ƙirar zamani.

Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi
Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun

Hotunan sun yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda mutane suka yi ta yaɗa hotunan cikin al'ajabin wannan tsoho wanda yaƙi yadda makamansa.

Idan ba a manta ba, Obasanjo ya mulki Najeriya a matsayinsa na soja tsakanin 1976 zuwa 1979.

An ƙara zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa na mulkin soji a watan Mayun 1999; kujerar da ya riƙe har 2007 kafin marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya amshi mulkin.

Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi
Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, za a ɗaure ƴan Najeriyan da suka ƙi yin rijistar ƴan ƙasa a gidan gyaran hali, don babu wanda zai mori romon damokradiyya ba tare da rijista ba a cewar ministan sadarwa, Dr Isa Pantami.

Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Pantami ya bayyana hakan a wani taro da suka yi na ministoci a gidan gwamnati dake Abuja.

Ya bayyana yadda aka yanke shawarar ta ɗaure marasa rijistar inda yace hakan ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasar nan don kada wani mara rijista ya mori romon demokraɗiiyya.

Pantami ya nuna muhimmancin samun lambar rijistar don sadata da layukan wayar mutum da kuma sauran ayyuka da yanzu aka wajabta dole sai an haɗa da ita lambar katin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel