Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige

Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige

- Gwamnatin Najeriya zata zartar da hukuncin dakatar da biyan likitoci matsawar basu yi aiki ba saboda yajin aikin da suka tsunduma

- Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ya bayar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a yayin da ake wata tattaunawa dashi

- A cewar Ngige, ma'aikatar kwadago tana da makaman da za ta yakesu kuma ta hukuntasu matsawar suka ki amincewa da tayin da ya gwamnati zata yi musu ranar Talata

Gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma'aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma'a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

"A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba," cewar Ngige.

KU KARANTA: Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga

Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige
Idan likitoci suka ki komawa aiki, za mu datse albashinsu, Chris Ngige. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

"Wadanda aka dauka aiki ya kamata su dage wurin kulawa da lafiyar marasa lafiya. Za mu iya neman likitocin gargajiya, bana fatan mu kai nan wurin amma in dai aka kai toh za mu yi amfani da tsumagiyarmu."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya jaddada matsayarsa na cewa Najeriya ta fi karfi tare da tsayuwa a matsayinta na kasa daya.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, a don haka yayi kira ga 'yan kasa da kada su bar masu bata musu suna su raba kasar nan.

Matsayar Buhari na kunshe ne a sakon ista wanda shugaban kasan ya taya 'yan Najeriya mabiya addinin Kirista murnar bikin, wanda Femi Adesina ya mika ga manema labarai.

Kamar yadda takardar ta sanar, "Kada mu bar masu bata suna sun yada zantuka marasa dadi domin kawo rabuwar kai ga 'yan kasa.

"Kamar yadda nace, mun fi zama tsayayyu kuma masu karfi a matsayinmu na kasa daya karkashin ikon Ubangiji.

“Ina taya 'yan uwana maza da mata murnar Ista da kuma fatan za a yi bikinta lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel