Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa

Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa

- Sojojin Najeriya sun bazama neman matuƙan jirgin saman da jirgin yaƙinsu yayi hatsari a dajin Sambisa a jihar Borno

- Yanzu haka sama da sa'o'i 24 kenan da faruwar lamarin kuma ba a ga matuƙin jirgin da abokan aikin shi ba

- Babu shakka ana fargabar mayaƙan Boko Haram na ƙarƙashin Sheƙau ne suka kai wa jirgin saman farmaki

Sojojin Najeriya sun bazama neman matuƙan jirgin sama da suka ɓata bayan an nemi wani jirgin yaƙi sama ko ƙasa ba a gani ba bayan jirgin ya tafka hatsari a dajin Sambisa dake arewa maso gabas na Najeriya.

HumAngle ta fahimci yadda sojojin suka rikice suna neman sojojin lungu da saƙon dajin Sambisa.

Yanzu haka an zarce sa'o'i 24 tun bayan faruwar lamarin.

Dajin Sambisa babban daji ne wanda yankin Boko Haram ɗin Sheƙau suka mamaye shi kuma ana zargin sune suka kaiwa jirgin farmaki.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke wadanda ake zargi da kaiwa Soludo hari

Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa
Ana cigaba da neman matukan jirgin saman sojin Najeriya da yayi hatsari a Sambisa. Hoto daga @DefenseInfoNG
Source: Twitter

KU KARANTA: Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya

Kamar yadda sojojin saman Najeriya suka sanar a takarda ranar Laraba, an rasa inda jirgin saman yake bayan fita ayyukan yau da kullum da yayi domin taimakawa dakarun sojin kasa.

An gano cewa aikin yana daga cikin kokarin dakarun na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso gabas.

Kamar yadda PRNigeria ta sanar, an ga jirgin yana yawo kusa da kauyukan Kurmiri da Njimia bayan ya ragargaji 'yan ta'adda a yankin Sambisa.

Kauyen Njimia dake kusa da dajin Sambisa na fuskantar aikin dakarun sojin saman da na kasa.

A wani labari na daban, za a ɗaure ƴan Najeriyan da suka ƙi yin rijistar ƴan ƙasa a gidan gyaran hali, don babu wanda zai mori romon damokradiyya ba tare da rijista ba a cewar ministan sadarwa, Dr Isa Pantami.

Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Pantami ya bayyana hakan a wani taro da suka yi na ministoci a gidan gwamnati dake Abuja.

Ya bayyana yadda aka yanke shawarar ta ɗaure marasa rijistar inda yace hakan ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasar nan don kada wani mara rijista ya mori romon demokraɗiiyya.

Source: Legit.ng

Online view pixel