Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara

Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara

- Wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun kai ziyara jihar Zamfara don yin jaje akan gobarar da ta auku a wata kasuwa

- Su Atiku Bagudu, Mai-Mala Buni da Gwamna Badaru sun je jaje musamman wurin gwamna Bello Matawalle

- Gwamnonin sun amince da dunkula N50,000,000 don tallafa wa masu karamin karfi da gobarar ta shafa

Wasu gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC sun wanke kafarsu musamman don kai ziyara jihar Zamfara don yin jaje ga jihar da jama'anta akan gobarar da ta tashi a babbar kasuwa jihar dake Tudun wada.

Shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya raka takwarorinsa daga jihar Yobe, gwamna Mai-Mala Buni tare da gwamna Badaru na jihar Jigawa har gidan gwamnati dake Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin wurin Gwamna Bello Matawalle.

Gwamna Bagudu ya tabbatar da yadda suka dade suna sanya ranar kai ziyara jihar Zamfara, duk da jam'iyyar PDP ce take mulkar jihar.

Channels TV ta ruwaito cewa, Matawalle ya koka akan gobarar da ta auku a kasuwar Tudun wada wacce ta janyo rashin walwala ga wadanda al'amarin ya shafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Tsohon mukaddashin gwamnan jihar Delta, Sam Obi, ya rasu

Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara
Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban kasan Japan ya nada 'ministan kadaici' bayan hauhawar kashe kai

A cewar gwamnan, wannan ziyarar ta tabbatar masa da yadda gwamnonin na APC suka nuna kulawa da tausayawa ga wadanda abin ya shafa.

Sun yaba wa gwamna Matawalle bisa kokarinsa na dawo da zaman lafiya jihar Zamfara, kuma yace gwamnonin APC sun amince da hada N50,000,000 don tallafa wa masu kananun karfin da gobarar ta shafa.

Gwamna Matawalle ya bayyana farin cikinsa bisa nuna kulawar da gwamnonin suka yi ta hanyar nikar gari har jihar Zamfara don nuna so da kauna garesu duk da bambancin siyasa dake tsakaninsu.

Ya nuna farin cikinsa duk da 'yan jam'iyyar PDP basu nuna masa irin wannan kaunar ba kuma ya tabbatar musu da cewa kofa a bude take idan zasu kai masa ziyara.

A wani labari na daban, alamu sun nuna cewa jirgin yakin sojojin Najeriya da ya bace an gan shi a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno mai nisan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Duk da hukumar rundunar sojin kasan bata riga ta tabbatar da wannan cigaban ba, majiyoyi a ranar Juma'a sun ce an ga jirgin yakin na shawagi a kauyukan Goni Kurmiri da Njimia bayan ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa da yayi.

Majiyoyin sun ce, har yanzu ba a samu labarin inda matukin jirgin da abokin aikinsa suke ba, Channels TV ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel